✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan PDP 6 a Majalisar Tarayya sun koma APC

 Ana yawan samun sauya sheka a Majalisar Wakilai daga jam'iyyun adawa zuwa APC mai mulki, a wannan majalisa ta 10.

Mambobin Jam’iyyar PDP shida a Majlisar Wakilai daga Jihar Delta sun sauya sheka zuwa Jam’iyya APC.

Kazalika wasu biyu daga Jihar Enugu sun sauya sheka daga Jam’iyyar adawa ta LP zuwa PDP.

Shugaban Majalisar Wakiliai, Abbas Tajuddeen, ne ya sanar da hakan bayan dawowar majalisar daga hutu a ranar Talata.

Shugaban Majalisar ya bayyana cewa ’yan majalisar sun yanke shawarar sauya sheka ne sakamakon rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyun nasu a matakin jiha da kuma kasa.

Wadanda sauka sauya sheka zuwa APC su ne: Victor Nwokolo,  Julius Pondi, Thomas Ereyitomi, Nicholas Mutu, Okodiko Jonathan, da kuma Nnamdi Ezechi. Wadanda suka bar LP zuwa PPD su ne Mark Obetta da kuma Dennis Nnamdi.

Idan ba ma manta ba a kwanakin baya ne Gwamnan Delta, Sheriff Francis Orohwedor Oborevwori, da tsohon gwamnan jihar kumwa tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa Ifeanyi Okowa, da wasu kusoshin PDP suka sauya sheka zuwa APC.

 Ana yawan samun sauya sheka a Majalisar Wakilai daga jam’iyyun adawa zuwa APC mai mulki, a wannan majalisa ta 10.