Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya buƙaci Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, da ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Matawalle ya yi wannan kira ne a ranar Asabar, a garinsu Maradun, yayin da dubban magoya bayansa suka kai ziyarar gaisuwar Sallah.
- Sallah: Gwamnatin Sakkwato ta bai wa kowane Alhaji kyautar N450,000
- Gwamnatin Tarayya na shirin farfaɗo da kamfanin ƙarafa na Ajaokuta
Matawalle, wanda shi ne tsohon gwamnan Jihar Zamfara, ya ce APC jam’iyya ce ta mutanen kirki da masu kishin ƙasa.
Ya ce maimakon a ci gaba da takun-saka tsakanin gwamnati da ’yan adawa, zai fi kyau Gwamna Dauda ya fito fili ya rungumi jam’iyyar da ke da madafun iko domin ci gaban jihar da ƙasar gaba ɗaya.
“Idan Gwamna Dauda na da niyyar kawo ci gaba musamman a fannin tsaro da zaman lafiya, babu laifi ya zo ya haɗu da sauran ’yan kwamitin ci gaba a APC,” in ji Matawalle.
Matawalle, ya jaddada cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ƙoƙari wajen samar da zaman lafiya da ci gaban ƙasa, kuma yana buƙatar goyon bayan gwamnonin jihohi da sauran shugabanni don cimma nasara.
A baya-bayan nan, wasu ’yan siyasa daga jam’iyyun adawa da dama sun sauya sheƙa zuwa APC.
Sun bayyana cewa suna son su haɗa kai da Gwamnatin Tarayya wajen samun mafita ga matsalolin da ƙasar ke fuskanta.
Wannan na ƙara wa APC ƙarfi a jihohi da dama, ciki har da Zamfara.
Kiran da Matawalle ya yi wa Gwamna Dauda Lawal da wasu shugabannin adawa na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar APC ke ƙara karɓar sabbin mambobi daga jam’iyyun adawa, a wani yunƙuri na ƙarfafa tsarin mulki.