✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‎Sarkin Katsinan Gusau ya rasu

‎Allah ya yi wa Sarkin Katsinan Gusau da ke jihar Zamfara, Dr Ibrahim Bello rasuwa.

‎Allah ya yi wa Sarkin Katsinan Gusau da ke jihar Zamfara, Dr Ibrahim Bello rasuwa.

Ya rasu da safiyar Juma’a a Abuja yana da shekaru 71, bayan ya sha fama da jinya.

Marigayin, wanda shi ne Sarkin Gusau na 16, ya ɗare kan karaga ne a shekara ta 2015, bayan rasuwar mahaifinsa.

Gogaggen ma’aikacin gwamnati, Dr Ibrahim ya taɓa zama Babban Sakatare a tsohuwar jihar Sakkwato da ma jihar Zamfara.

‎Ya yi mulkin ne na tsawon shekara 10 da ’yan watanni kafin rasuwar tasa.

Da yake tabbatar da rasuwar, Kakakin Gwamna Dauda Lawal na jihar ta Zamfara, Sulaiman Idris, a jajanta wa mutanen jihar a kan rasuwar.

A cikin wata sanarwa da safiyar Juma’a, Gwamnan ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi a wajensa, inda ya ce Sarkin ya tsaya tsayin daka wajen ci gaban jihar.

Daga nan sai ya yi addu’a Allah ya jikan mamacin ya kuma ba iyalansa da ma al’ummar jihar haƙurin jure rashin sa.