Kwamitin zartaswa na Jam’iyyar APC na ƙasa ya naɗa Ministan Jin-ƙai da Yaƙi da Talauci, Farfesa Nentawe Yilwatda, a matsayin sabon shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa.
Nan take aka rantsar da Nentawe Yilwatda a wajen taron.
- Kwalara: Mutum 13 sun mutu sama da 236 na jinya a Neja
- Jirgin Rasha mai dauke da mutum 50 ya yi hatsari a China
Nentawe ya yi rantsuwar ne da misalin ƙarfe 02:50 na rana a gaban manyan jiga-jigan jam’iyyar yayin taron NEC karo na 14 da ya gudana a ɗakin taro na fadar gwamnati da ke Abuja, ranar Alhamis.
Nentawe, wanda ya fito daga Jihar Filato, shiyyar Arewa ta Tsakiya, shi ne ɗan takarar Gwamna na Jam’iyyar APC a zaɓen 2023.