✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nentawe Yilwatda ne zai zama sabon shugaban APC na ƙasa

Matukar ba a sami sauyin tsare-tsare ba, akwai yiwuwar Ministan Jinkai da Yaki da Talauci, Farfesa Nentawe Yilwatda ya zama sabon shugaban jam’iyyar APC na…

Matuƙar ba a samu sauyin tsare-tsare ba, akwai yiwuwar Ministan Jin-ƙai da Yaƙi da Talauci, Farfesa Nentawe Yilwatda ya zama sabon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa a yau Alhamis.

Majiyoyi da dama a daren jiya sun shaida wa Aminiya cewa Nentawe ne ke kan gaba a cikin mutanen da ake so su ɗare shugabancin jam’iyyar mai mulki.

Sai dai a cewar wasu majiyoyin, tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Umaru Tanko Almakura, shi ma na daga cikin waɗanda ake duba yiwuwar bai wa kujerar.

A daidai lokacin da ya rage ’yan sa’o’i gabanin taron Kwamitin Zartarwa na jam’iyyar, majiyoyi da dama sun shaida cewa shugabancin jam’iyyar, wanda ya ƙunshi Shugaban Ƙasa da Gwamnoni sun yanke shawarar taƙaita neman wanda zai hau kujerar tsakanin Nentawe da Almakura.

Nentawe dai ɗan asalin Jihar Filato ne, da ke shiyyar Arewa da Tsakiya, yankin da aka tsara zai fitar da shugaban jam’iyyar kafin daga bisani aka naɗa tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya ajiye muƙaminsa a farkon wannan watan.

Sai dai majiyoyin sun ce an saka sunan Almakura ne a matsayin zaɓi na biyu.

Tun bayan saukar Ganduje dai ’yan shiyyar Arewa ta Tsakiya ke ta hanƙoron ganin an dawo da kujerar yankinsu, kasancewar ɗan cikinsu, wato Sanata Abdullahi Adamu ne ke kanta kafin ya sauka bayan nasarar Shugaba Tinubu a zaɓen 2023.

Bayanai sun nuna sai da aka yi dogon nazari kafin a yanke shawarar fauko ɗan yankin kuma Kirista, saboda a haƙurƙurtar da waɗanda zaɓin Musulmai guda biyu, Tinubu da Kashim, ya baƙantawa rai.

Duk wanda ya yi nasarar dai shi ne zai karɓi ragamar da shugabanta na riƙo na yanzu, Ali Bukar Dalori, wanda mataimakin shugaba ne kafin saukar Ganduje.

Wasu dai na cewa da shi aka ƙyale ya ci gaba, amma wata majiyar ta ce kasancewarsa daga jiha ɗaya da Shettima sannan kuma Tinubu na so a yi ta ta ƙare kan batun shugabancin ya sa dole a zaɓo wani.

Wata majiyar kuma ta ce, “Tinubu na san wani ɗan-a-mutun shi ya zama shugaban kamar yadda Abdullahi Adamu ya kasance zamanin Buhari”.

Sauran waɗanda a baya aka yi ta raɗe-raɗin za su hau kujerar sun haɗa da Sanata Sani Musa (Neja) da Sanata Salihu Mustapha (Kwara) da Sanata Joshua Dariye (Filato) da Sanata George Akume (Binuwai) da kuma Sanata Abu Ibrahim (Katsina).