Friedrich Merz na jam’iyyar CDU ya zama sabon shugaban gwamnatin Jamus.
Majalisar Dokokin Jamus ta Bundestag ta zabi Merz a matsayin sabon shugaban gwamnati lokacin zaɓen zagaye na biyu, bayan ya gaza samun ƙuri’un da yake buƙata a zagayen farko na zaɓen.
A zaɓen farko Merz ya samu ƙuri’u 325 na jam’iyyun ƙawance daga majalisar mai mambobi 630.
Kafin zama shugaban gwamnati ana buƙatar kuri’u 316 kuma jam’iyyar CDU/CSU da kuma jam’iyyar SPD suna da kujerun majalisar 328, fiye da adadin da ake buƙata.
Merz zai maye gurbin Olaf Scholz wanda ya faɗi zaɓen ƙasar da aka gudanar a watan Fabrairu
Da yake sanar da soma kaɗa ƙuri’u a zagaye na biyu, shugaban ƙungiyar Tarayyar Turai a majalisar, Jens Spahn, ya ce, “Gaba ɗaya nahiyar Turai, wataƙila ma duniya baki ɗaya, na kallon wannan zagaye na biyu na zaɓen.”
Jamus wadda ke zaman ƙasa mafi yawan al’umma a cikin ƙasashe 27 na Tarayyar Turai, ita ce ke da mafi girman tattalin arziƙin nahiyar kuma a sahun farko ta fuskar diflomasiyya.
A yanzu dai ajandar da Mista Merz zai sanya a sahun farko sun haɗa da yaƙin da ake yi a Ukraine da kuma manufofin da gwamnatin Donald Trump ta shimfiɗa kan harkokin kasuwanci ƙari kan al’amuran cikin gida, kamar tasowar jam’iyyar masu ra’ayin mazan jiya, mai ƙyamar baƙin haure.