✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Al’ummar Jamus sun raba shanun Layya 700 a Kano

Kanawa 5,600 sun amfana da naman layyan shanu 700 da al'ummar Jamus suka yanka a fadin a Babbar Sallah bana

Al’ummar kasar Jamus sun raba wa Kanawa 5,600 naman layyan shanu 700 da suka yanka a fadin jihar a Babbar Sallah bana.

Kungiyar jinkai ta HASENE daga kasar Jamus da kuma Gidauniyar BARIS ne suka bayar da gudummawar shanun layyan domin taya Kanawa bikin Sallar Layya.

Daya daga cikin wadanda suka ba da shanu layyan, Muhammad Aydin, ya ce sun yi bikin Babbar Sallar bana a Kano ne da nufin kara kulla dangon ’yan uwantakan Musulunci tsakaninsu da al’ummar Kano.

Muhammad ya kuma bisa kyakkyawar tarbar da suka samu daga al’ummar Kano da ma gwamnatin jihar.

Da yake jagorantar rabon naman da aka kaddamar a Jami’ar Bayero ta Kano, Gwamnan Abba Kabir Yusuf, ya bayyana godiyar gwamnatin jihar bisa gudunmmawar da ta sanya wa mabukata farin ciki a lokacin bikin sallar.

Gwamna Abba ya umarci jami’an da aka dora wa alhakin kula rabon naman da su tabbatar da cewa marasa lafiya da ke sibitoci da fursunoni da kuma mabarata sun samu.

Sannan ya ja hankalinsu da su yi adalci a wurin rabon domin ganin an cimma manufar layya da kuma sauke nauyin amanar da aka dora musu.