Gwamnatin Jamus ta ce tana ci gaba da samun galaba na daƙile kwararar baƙin haure masu shiga ƙasar tare da mayar da wadanda aka yi watsi da takardunsu na neman mafaka zuwa inda suka fito.
Ministar harkokin cikin gida ta Jamus, Nancy Faeser, ta bayyana cewa gwamnatin ƙasar mai barin gado ta taka muhimmiyar rawa wajen daƙile shigar baƙin haure cikin ƙasar.
- Tinubu ya cire Mele Kyari daga shugabancin NNPC
- DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Arewa Ke Tafiya Kudu Farauta
Faeser ta ce gwamnatin na ci gaba da daukan matakin mayar da baƙin haure ƙasashen da suka fito, inda yanzu haka aka samu raguwar masu ajiye takardun neman mafaka a ƙasar, mafi ƙarfin tattalin arziki tsakanin ƙasashen Turai.
Faeser ta ce gwamnatin da Olaf Scholz ke jagoranta ta aiwatar da manufofi masu tasiri da suka taimaka wajen daƙile shigar baƙin haure zuwa ƙasar Jamus.
Nancy Faeser ’yar jam’iyyar SPD mai mulki za ta ajiye muƙamin na ministar cikin gida da zarar an kafa sabuwar gwamnati, bayan zaɓen da jam’iyyar CDU ta kasance a matsayi na farko wanda aka yi ranar 23 ga watan Fabrairun wannan shekara ta 2025.
Ana sa ran Friedrich Merz na jam’iyyar CDU ya zama shugaban gwamnatin na gaba da za a kafa a ƙasar ta Jamus.