Gwamnatin Nijeriya ta ce tattaunawa ta yi nisa domin kwaso ’yan ƙasar guda 15,000 da suke gudun hijira a ƙasashen Kamaru da Nijar da Chadi da wasu ƙasashen cikin mutunci.
Kwamishinan hukumar kula da ’yan gudun hijira ta Nijeriya, Alhaji Tijjani Ahmed ne ya bayyana haka a zantawarsa da manema labarai a Abuja.
- Matakan da gwamnonin Arewa suke so a ɗauka kan matsalar tsaron yankin
- An kama matashi da kawunan mutanen a Legas
Ya ce akwai aƙalla ’yan Nijeriya miliyan shida da ke zaman gudun hijira a cikin ƙasar, sannan akwai wasu dubbai da suke zaune a wasu ƙasashen na duniya.
“Akwai ’yan Nijeriya 15,000 da suke so su dawo da kansu; haka kuma muna da ’yan ƙasashen waje aƙalla 100,000 da suke zaman gudun hijira a ƙasar nan.
“Dukkan mutanen nan suna da alhaki a hukumarmu na ba su kulawar da ta dace,” in ji shi.
Ahmed ya yi godiya ga Shugaban Bola Tinubu bisa gudunmuwar da yake ba ma’aikatar jinƙai, sannan ya nanata ƙudurinsu na tabbatar da kwaso ’yan ƙasar da ke zaune a wasu ƙasashen.