Akalla mutane 20 sun mutu yayin da wasu 16 suka jikkata a wani rikicin ƙabilanci da ya auku a wani lardi na gabashin kasar Chadi.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar sadarwa ta ƙasar ta fitar, ta ce fadan ya barke ne daga ranar 10 zuwa 14 ga watan Yuni a yankin Molou na lardin Ouaddai da ke gabashin kasar.
- An garzaya da ’yan Isra’ila 154 asibiti bayan harin Iran
- Tankokin Isra’ila sun kashe mutum 51 a wurin karbar abinci a Gaza
Wata majiya ta ce rikicin ya samo asali ne bayan da matasan Zaghawa biyu dauke da makamai suka sace babur na wani dan kabilar Ouaddai a ranar Talata, lamarin da ya haddasa kazamin rikici.
Bayanai sun ce rikicin ya yi kamari ne a ranar Asabar lokacin da aka kashe akalla ‘yan kabilar Ouaddai 12 a wani hari da ‘yan kabilar Zaghawa suka kai.
Kazalika, wata sanarwa da suka fitar a birnin N’djamena, ’yan majalisar dokoki 14 na lardin Ouaddai, sun yi Allah wadai da abin da suke danganta da munanan ayyuka, tare da yin kira ga hukumomin kasar da su kara kokarin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin ’yan kasar.
Tun dai shekaru da suka wuce ne, gabashin Chadi da ke kan iyaka da Sudan ke fama da rikici tsakanin manoman kabilar Ouaddai da kuma kabilun Larabawa, wadanda makiyaya ne.