An shiga ruɗu da fargaba a garuruwan ƙasar Chadi da dama, sakamakon jita-jita da kafofin sada zumunta na yanar gizo ke yaɗawa cewa wasu matsafa na satar al’aurar maza.
Tun daga birnin Moundou da ke kudancin kasar da lamarin ya fara samun asali, inda wasu matasa hudu suka yi ikirarin cewa an sace musu al’aurarsu ta hanyar bakar tsafi, na yaduwa kamar wutar daji a wasu manyan biranen ƙasar Chadi.
Sakamakon jita-jita da bidiyoyi iri-iri da ake yadawa a shafukan sada zumunta, duk da cewa ba a tabbatar da wannan zargi a likitanci ko a hukumance ba, lamarin ya bazu tare da tada hankula har a tsakiyar N’Djamena, babban birnin kasar, inda wasu fusatattun mutane suka yi yunkurin kashe wani mutum wanda suka zarga da sace al’aurar wasu yara maza uku bayan ya yi musabaha da su, sai dai ya tsira da ransa sakamakon shiga tsakani da ’yan sanda suka yi, amma ya ji jiki da ɗan karen duka.
Babu tushe a zahiri
A yayin da ake fuskantar wannan al’amari wanda a halin yanzu girmansa na iya haifar da hargitsi na zaman lafiyar jama’a, gwamnati ta yanke shawarar tashi tsaye don ƙoƙarin kawo karshensa.
Kakakin gwamnatin Chadi, Gassim Cherrif ya ce lamarin na neman wuce gona da iri, domin kuwa ana kai wa mutane hari tare da jikkata da dama saboda zargi marasa tushe a zahari, yana mai cewa gwamnati ba za ta zuba ido tana gani har lamarin ya girma ba, ta yadda mutane ke ɗaukar doka da hannunsu.