✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kai hari Fadar Shugaban Ƙasar Chadi

A ranar Laraba ne mayaƙan Boko Haram suka sheka lahira bayan sun kai hari Fadar Shugaban Ƙasa Chadi da ke birnin N’Djamena

Dakarun sojin kasar Chadi sun halaka mayaƙan Boko Haram da dama tare da kama wasu bayan harin da ƙungiyar ta kai Fadar Shugaban Ƙasar.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa mayaƙan sun kai hari a cikin harabar Fadar Shugaban Ƙasar da yammacin ranar Laraba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito cewa jerin gwanon motocin sojoji sun nufi  Fadar Shugaban Ƙasa, a yayin da aka tare hanyar.

Mayaƙan Boko Haram sun gamu da ajalinsu bayan sun ƙaddamar da mummunan harin a birnin N’Djamena.

Wani bidiyo da aka wallafa a kafofin sada zumunta ya nuna sojojin suna yi musu ruwan wuta, a yayin da rahotanni ke nuni da cewa an kama wasu daga cikin mayakan suna amsa tambayoyi.

A yammacin ranar Laraba ne mazauna birnin N’Djamena suka shiga zaman ɗar-ɗar bayan sunfara jin ƙarar harbe-harbe a kusa da fadar shugaban ƙasar.

Sai dai daga bisani, Ministan Ababen More Rayuwa na ƙasar, Aziz Mahamat Saleh, ya sanar da cewa an shawo kan lamarin. Ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, “ba wani abin damuwa ba ne, an riga an magance matsalar.”

Wani jami’in gwmanatin ƙasar, Abderaman Koulamallah, ya ce, “wata ’yar matsala cewa…komai ya daidaita.

Ya wallafa wani bidiyo a Facebook da ya ce an ɗauka a fadar shugaban ƙasan ne, inda ya ƙara da cewa, “an murƙushe ɗauƙacin yunkurin na tayar da zaune tsaye a ƙasar.”