✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe sojoji 12 a barikin Nijar

An cafke mutane biyu da ake zargi da kai hari barikin sojojin da ke da nisan mil shida daga ƙauyen Sakoira.

An kashe sojoji 12 a yankin Tillaberi na yammacin ƙasar mai iyaka da Mali da Burkina Faso, yankin da ke zama tungar masu iƙirarin jihadi da ’yan ina da kisa masu nasaba da ’yan ƙungiyoyin al Qaeda da IS.

Ma’aikatar tsaron Nijar ta sanar da cewa an yi wa dakarunta na bataliyar ko-ta-kwana mai suna Almahao kwanton ɓauna ne a wani kauye da ke kusa da Sakoira na yammacin Tillaberi, inda sojan suka jima suna ɓarin wuta da ’yan ta’adda kafin a kawo musu ɗauki.

Gwamnatin ta bayyana cewa tuni ta cafke mutane biyu da ake zargi da kai harin a barikin sojojin da ke da nisan mil shida daga ƙauyen Sakoira a jihar ta Tillaberi.

A baya gwamnatin ƙasar ta sanar da kashe ’yan ta’adda tara, ta kuma ƙwace makamai daga hannu masu iƙirarin jihadi da suka kai wani harin da ta daƙile a yankin.

A yankin Tahoua mai iyaka da Nijeriya, rundunar tsaron Nijar ɗin ta sanar da ɗauki ba dadi da Lakurawa masu yawan yin kutse kuma suna kai hari ga bututun man fetur ɗinta da ke zuwa gaɓar teku a Benin.

Nijar Mali da kuma Burkina faso sun shafe sama da shekaru 10 ƙarƙashin barazanar ƴan ta‘adda masu iƙirarin jihadi da ke afkawa jami’an tsaro da kuma fararen hula lokaci zuwa lokaci.

To sai dai kuma ƙididdiga ta nuna ƙaruwar kai hare-hare tun bayan da sojojin ƙasashen uku suka yanke shawarar kifar da gwamnatin fararen hula.

Rikicin yankin Sahel da ya samo asali daga ƙasar Mali a 2012, wanda kuma ya faɗaɗa har zuwa ƙasashen Burkina Faso da Nijar da kuma Benin da ya halaka dubban mutane kama daga sojoji har zuwa farar hula.