Aƙalla Falasɗinawa 13 ne suka rasu a ranar Asabar a Gaza, sakamakon hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai.
Mutum shida daga cikinsu sun mutu ne a kusa da cibiyar rabon tallafi a garin Rafah da ke Kudancin Gaza.
- 2027: Makomar Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu na janyo cece-kuce
- Yadda Sanusi II da Aminu Ado suka yi sallar Idi daban-daban a Kano
Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta Gaza, Mahmud Bassal, ya ce harin ya faru da misalin ƙarfe 7 na safe, a kusa da gadar Al-Alam.
Mutane sun taru a wajen domin karɓar tallafi daga wata cibiya da Gidauniyar Gaza Humanitarian Foundation (GHF) ke jagoranta, wadda ke samun goyon bayan Amurka, kimanin kilomita ɗaya daga wajen.
Shaidu sun ce, da zarar wasu suka yi ƙoƙarin matsawa kusa da cibiyar agajin, sai sojojin Isra’ila da ke cikin motocin yaƙi su fara harbi a sama, kafin daga baya suka buɗe wa mutane wuta.
Dakarun Isra’ila sun ce suna bincike kan lamarin.
Wannan ba shi ne karon farko da aka kashe mutane a kusa da cibiyar agaji ta Al-Alam ba.
Gidauniyar GHF ta fara rabon tallafin ne tun ƙarshen watan Mayu, bayan Isra’ila ta sassauta wani takunkumi da ta ɗora wa Gaza na sama da watanni biyu.
Majalisar Ɗinkin Duniya dai ta ƙi haɗa kai da GHF saboda rashin tabbas kan adalci, kuma ta yi gargaɗin cewa kusan dukkanin al’ummar Gaza sama da mutum miliyan biyu na fuskantar barazanar yunwa.
A wani ɓangare na Gaza a ranar Asabar, an kuma kashe mutum bakwai sakamakon wani hari da jirgin saman Isra’ila ya kai wani gida kusa da Asibitin Al-Shifa da ke birnin Gaza.
Sojojin Isra’ila sun ce shi ma za su binciki wannan harin.