✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Slovenia ta sanya wa ministocin Isra’ila 2 haramcin shiga ƙasar

Slovenia ta bayyana cewa wannan shi ne karon farko da wata ƙasa a Turai ta dauki wannan mataki.

Gwamnatin Slovenia ta sanya wa wasu ministocin Isra’ila biyu haramcin shiga ƙasar bayan samunsu da hannu dumu-dumu wajen keta haƙƙin bil Adama a kan Falasdinawan Zirin Gaza.

Kafofin watsa labaran Turai sun ruwaito cewa wadanda haramcin ya shafa sun hada da Ministan Tsaron Isra’ila Itamar Ben Gvir da takwaransa na Kudi Bezalel Smotrich.

Ministar Harkokin Wajen Slovenia, Tanja Fajon ta sanar da manema labarai a ranar Alhamis cewa wannan shi ne karon farko da wata ƙasa a Turai ta dauki wannan mataki.

Tun da fari dai, Shugabar Slovenia, Natasa Pirc Musar, ta sanar da zauren majalisar dokokin EU cewa lokaci ya yi da ya kamata a taka wa Isra’ila birki a kisan kiyashin da take yi a Gaza.

Ko a watan Yunin 2025, ƙasashen Australiya da Kanada da Birtaniya da New Zealand da kuma Norway sun dauki makamancin wannan mataki na haramta wa Smotrich da Ben Gvir, da ke kasancewa ƙusoshin gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu shiga ƙasashen.