Sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa 24 daga cikin dare zuwa wayewar garin ranar Alhamis a Zirin Gaza.
Majiyoyi a yankin sun shaida wa gidan talabijin na Al-Jazeera cewa akasarin mutum 24 din da aka kashe a zirin na Gaza mata ne da kananan yara.
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata
- Ba Tinubu kaɗai ne ya sa Buhari ya ci zaɓe a 2015 ba – Boss Mustapha
Akasarin mutanen dai an kashe su ne a tsakiya da kudancin zirin na Gaza.
Ma’aikatan lafiya a asibitin Al-Aqsa da ke Gaza sun ce a yankin Deir el-Balah kawai akwai Falasdinawa 13 da aka kashe sannan an jikkata wasu da dama.
Gabanin nan ma, Isra’ila ta kashe mutum hudu a harin da ta kai sansanin ’yan gudun hijira na Bureij, shi ma wanda ke tsakiyar Gaza.
Sama da mutum 700 ne Isra’ila ta kashe Falasdinawa 700 da ke kokarin karbar tallafi a wuraren karbar tallafi na Gidauniyar GHF wanda Amurka da Isra’ilar suke goya wa baya tun lokacin da aka kaddamar da shi a watan Mayu.
Daga cikin mutanen dai akwai yara kanana da dama, ciki har da wani jariri dan kwana 10 da haihuwa.