Friedrich Merz na jam’iyyar CDU ya zama sabon shugaban gwamnatin Jamus.
Majalisar Dokokin Jamus ta Bundestag ta zabi Merz a matsayin sabon shugaban gwamnati lokacin zaɓen zagaye na biyu, bayan ya gaza samun ƙuri’un da yake buƙata a zagayen farko na zaɓen.
A zaɓen farko Merz ya samu ƙuri’u 325 na jam’iyyun ƙawance daga majalisar mai mambobi 630.
Kafin zama shugaban gwamnati ana buƙatar kuri’u 316 kuma jam’iyyar CDU/CSU da kuma jam’iyyar SPD suna da kujerun majalisar 328, fiye da adadin da ake buƙata.
Merz zai maye gurbin Olaf Scholz wanda ya faɗi zaɓen ƙasar da aka gudanar a watan Fabrairu
Upon announcing the second vote, the head of the Union bloc in parliament, Jens Spahn, said, “The whole of Europe, perhaps even the whole world, is watching this second round of elections.”
Da yake sanar da maimaita kaɗa ƙuri’u a zagaye na biyu, shugaban ƙungiyar Tarayyar Turai a majalisar, Jens Spahn, ya ce, “Gaba ɗaya nahiyar Turai, wataƙila ma duniya baki ɗaya, na kallon wannan zagaye na biyu na zaɓen.”
Jamus wadda ke zaman ƙasa mafi yawan al’umma a cikin ƙasashe 27 na Tarayyar Turai, ita ce ke da mafi girman tattalin arziƙin nahiyar kuma a sahun farko ta fuskar diflomasiyya.
A yanzu dai ajandar da Mista Merz zai sanya a sahun farko sun haɗa da yaƙin da ake yi a Ukraine da kuma manufofin da gwamnatin Donald Trump ta shimfiɗa kan harkokin kasuwanci ƙari kan al’amuran cikin gida, kamar tasowar jam’iyyar masu ra’ayin mazan jiya, mai ƙyamar baƙin haure.