✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bruno Labbadia ya yi watsi da aikin horas da Super Eagles

’Yan hana ruwa gudu ne suka sa muka soke yarjejeniyar da aka kulla da Labbadia.

Kocin nan ɗan ƙasar Jamus, Bruno Labbadia, ya yi watsi da yarjejeniyar horas da tawagar Super Eagles saboda gazawar Hukumar Kwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF) wajen cimma matsaya kan biya masa haraji.

Wata sanarwa da NFF ta fitar, ta ce tsauraran ka’idoji na hukumomin harajin Jamus da kuma haɗin bakin wasu ’yan hana ruwa gudu ne dalilan soke yarjejeniyar da ta kulla da Labbadia.

NFF ta ce hukumomin na Jamus sun yi wa Labbadia matsin lambar rasa wannan aiki sakamakon buƙatar da suka gabatar ta neman Nijeriya ta riƙa biyan ƙarin kaso 32 zuwa 40 na albashinsa a matsayin haraji.

A bayan nan ne Hukumar ta NFF ta sanar cewa ta cimma matsaya da Labbadia dan asalin kasar Jamus, wanda zai zama koci na 37 da zai horar da ‘yan wasan na Nijeriya.

Sai dai NFF ta ce babu batun biya masa haraji a cikin ƙunshin yarjejeniyar da ta kulla da Labbadia kafin amincewa da tayin da ta yi masa.

A halin yanzu, Kociya Augustine Eguavoen ne zai ci gaba da jan ragamar horas da tawagar Super Eagles a yayin da take shirin tunkarar wasannin neman gurbin shiga Gasar Kofin Nahiyyar Afirka da za ta fafata da Jamhuriyar Benin da kuma Rwanda duk a watan Satumba.

Wannan zai zama karo na huɗu ke nan da Eguavoen zai jagoranci horas da tawagar Super Eagles bayan aikin da ya yi a tsakanin 2005 zuwa 2007 da 2010 da kuma 2022.