✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar wakilai na shirin ƙwace rajistar jam’iyyu daga hannun INEC

Ƙudirin na son a kafa hukumar da za ta kula da rajistar jam'iyyu da kuma al'amuransu.

Majalisar Wakilai na shirin kafa wata sabuwar hukuma da za ta karɓi ikon yin rajistar jam’iyyun siyasa daga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).

Wannan na zuwa ne bayan da majalisar ta gabatar da wani sabon ƙudiri kan batun.

Kakakin Majalisar, Hon. Tajudeen Abbas, tare da Hon. Marcus Onobun daga Jihar Edo ne, suka gabatar da ƙudirin.

Ƙudirin na neman kafa wata hukuma mai zaman kanta da za ta riƙa yi wa jam’iyyu rajista, kula da dokokinsu, da kuma tallafa musu.

Har ila yau, ƙudirin na neman a kafa wata kotu ta musamman da za ta duba ƙorafe-ƙorafen da suka shafi jam’iyyu da rikice-rikicen da ke tasowa a tsakaninsu.

A cewar Hon. Marcus Onobun, wannan matakin ya zama dole domin kawo ƙarshen rikice-rikicen cikin gida da ke addabar jam’iyyun siyasa a Najeriya.

A halin yanzu, ƙudirin ya tsallake karatu na biyu a majalisar, lamarin da ke nuni da cewa ana iya ci gaba da duba yiwuwar aiwatar da shi a nan gaba.