✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin APC ta jefa ’yan Najeriya cikin ƙangin talauci — Shugabar LP

Shugabar ta nemi 'yan Najeriya su goya wa jam'iyyar LP baya a babban zaɓe mai zuwa.

Muƙaddashiyar Shugabar Jam’iyyar LP, Sanata Nenadi Esther Usman, ta ce gwamnatin APC ce ta fi jefa ’yan Najeriya cikin talauci sama da kowace gwamnati a tarihin ƙasar nan.

Da ta ke zantawa da manema labarai a Jihar Kaduna, Sanatan ta ce jam’iyyar LP ta shirya tsaf don gyara kurakuran da gwamnatin APC ta tafka.

Ta roƙi ’yan Najeriya da su bai wa LP goyon baya, inda ta ce jam’iyyar za ta kawo canji na gaskiya.

Ta ce halin da ake ciki na wahala a ƙasar nan ya yi muni ƙwarai, kuma ta d6ora alhakin hakan kan gwamnatin APC.

Game da sauya sheƙa da wasu ’yan siyasa ke yi daga jam’iyyun adawa zuwa APC, ciki har da wasu daga LP, Sanatan ta bayyana hakan a matsayin abin takaici da rashin sanin darajar kai.

A cewarta, ba daidai ba ne mutum ya samu madafun iko da tallafin wata jam’iyya, amma daga baya ya koma wata jam’iyya don kawai samun riba ba.

Sai dai ta ce wannan ba zai girgiza jam’iyyarsu ba, domin ƙarfin jam’iyyar na ƙara bayyana da goyon bayan talakawan Najeriya.

Sanata Esther ta amince cewa jam’iyyar ta yi wasu kurakurai a baya, musamman wajen zaɓen ’yan takara da ba su dace da manufofin jam’iyyar ba.

Amma ta tabbatar da cewa sun ɗauki darasi, kuma suna shirin yin gyara kafin babban zaɓe na gaba.

“Yawancin waɗanda suka bar jam’iyyar ba su da cikakken ƙudirin kafa sabuwar Najeriya. Ficewarsu ta sa mun fi fahimtar juna kuma ta ƙara mana ƙarfi,” in ji ta.

Ta roƙi mambobin jam’iyyar da aka ɓata ws raj da su manta da saɓanin, su haɗa kai domin ƙarfafa jam’iyyar.

Ta ce ana shirin gudanar da zaɓen shugabanni a matakin ƙasa da kuma babban taron ƙasa kuma Majalisar Zartarwar Jam’iyyar (NEC) ta amince da waɗannan sauye-sauye da suke buƙata.