✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

LP za ta ceto Nijeriya daga halin da APC ta jefa ta — Nenadi Usman

Ficewar mambobin jam’iyyar LP tana ƙara mana ƙwarin gwiwa da kuma fayyace mana masu kishin jam’iyyar na gaskiya.

Shugabar riƙo ta jam’iyyar Labour (LP) ta ƙasa, Sanata Nenadi Usman, ta ce jam’iyyarsu ta shirya tsaf domin gyara manyan kura-kurai da gazawar da gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki ta jefa Nijeriya a ciki.

Sanata Usman ta bayyana hakan ne a wata ganawa da manema labarai a ƙarshen mako a Jihar Kaduna dangane da abinda da ke faruwa a cikin jam’iyyar LP.

Sanatar ta buƙaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da goya musu baya domin a cewarta, jam’iyyar LP ce za ta farfaɗo da fatan da al’umma ke da shi da kuma ɗaga martabar ƙasar nan.

A cewarta, “Gwamnatin APC ta fi kowacce gwamnati a tarihin kasar nan jefa talakawan Nijeriya cikin ƙuncin rayuwa da fatara.”

Dangane da sauya sheƙa da ‘yan siyasa ke yi daga jam’iyyun adawa zuwa jam’iyyar APC mai mulki, ciki har da wasu daga cikin ‘yan LP, Sanata Usman ta bayyana hakan a matsayin abin takaici, inda ta bayyana shi a matsayin abin kunya ne mutum ya samu nasara a cikin wata jam’iyya sannan ya canza sheƙa zuwa wata jam’iyyar.

Sai dai ta ce jam’iyyar LP ba ta damu da waɗannan sauya sheƙar ba, matuqar jama’ar ƙasa na tare da ita.

“Karfinmu yana fitowa ne daga goyon bayan talakawan Nijeriya, ba daga mahandama masu son kansu ba.”

Sanata Usman ta yarda cewa jam’iyyar ta aikata kura-kurai, musamman wajen tsayar da ‘yan takarar da ba su da cikakken fahimta ko biyayya ga manufofin jam’iyyar, amma ta tabbatar da cewa irin wannan kuskure ba zai maimaitu ba a nan gaba.

“Da yawa daga cikin waɗanda suka fice daga jam’iyyar tun farko ba su da cikakkiyar fahimta kan akidar gina sabuwar Nijeriya.

“Ficewarsu tana ƙara mana ƙwarin gwiwa kuma hakan yana fayyace mana masu kishin jam’iyyar na gaskiya,” inji ta.

Ta kuma buƙaci dukkan ‘ya’yan jam’iyyar da ke da saɓani da su rungumi sulhu su haɗa kansu yayin da jam’iyyar ke shirin ƙaddamar da sabunta rajistar mambobinta, gudanar da tarukan gunduma da na jihohi, da kuma babban taron ƙasa wanda tuni an samu amincewa daga Kwamitin Zartaswa na Kasa (NEC).