Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya karɓi baƙuncin Julius Abure, ɗaya daga cikin shugabannin jam’iyyar LP, a gidansa da ke Abuja.
Zuwa yanzu dai ba a san dalilin wannan ganawa ba, amma mutane da dama sun fara surutu da hasashen abin da shugabannin suka tattauna.
- Matsalar tsaro na raguwa, tattalin arziƙi na farfaɗowa — Sanata Adaramodu
- Haɗakar ’yan hamayya alheri ce ga siyasar Nijeriya — Gbajabiamila
Wike wanda yake ɗan jam’iyyar PDP, amma a yanzu yana aiki a Gwamnatin jam’iyyar APC.
An zargi Julius Abure da yi wa jam’iyyarsa ta LP zagon ƙasa, amma ya musanta waɗannan zarge-zarge.
Lere Olayinka, mai magana da yawun Wike, ne ya yaɗa hotunan wannan ganawa a ranar Lahadi.
Ga hotunan ganawar a ƙasa: