✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda gwamnati ta yi wa noman alkama rikon sakainar kashi

Koyaushe gwamnantin za ta dauki matakin da ya dace wajen noman alkama?

Yayin da lokacin soma shukar alkama yake dada karatowa, manoma musamman na Jihar Kano sun fara kokawa dangane da nuna halin ko-in-kula na gwamnati ke yi kan yadda ake noman a kasar, duk da wagegen gibi da ake da shi da ya kamata cike shi.

Manoman alkamar da wakilinmu ya zanta da su, sun yi ikirarin cewa, idan har ana so a wadata kasar da shinkafa da kuma wannan hatsi mai daraja sai Gwamnatin Tarayya ta sake duba manufofinta, ta yadda za ta bayar da damar da za a yi noman yadda ya kamata.

Alhaji Usman Bashir, manomin alkama ne a Jihar Kano, a hirarsa da wakilinmu ya bayyana bakin cikinsa a kan yadda noman alkama yake ja da baya da kuma yadda gwamnati ta nade hannunta ta kyale manoman suke fuskantar matsalolin su kadai.

Ya ce kamata ya yi a sake duba manufofin gwammati kan noman alkamar baki dayansa kamar yadda aka yi na Shinkafa. Kuma a yi hakan cikin gaggawa.

A cewarsa, abin da ya faru bayan annobar Kwarona, Hukumar Kula da Bincike Ayyukn noma na Tafkin Chadi suka daina rarraba wa manoma ingantattun irin shuka na alkama.

“A shekaru da suka wuce kowane manomi jira ya ke yi Cibiyar Binciken ta Tafkin Chadi ta ba shi Irin shuka. Soboda ita ce Cibiyar Bincike ta hakuma da ta ke da cikakken ikon yin haka.

“Kuma manoma sun fi gamsuwa da irin agajin da ta ke bayarwa a wannan fanni.

“Sai dai wani abin takaici shi ne, tun waki’ar da ta faru ta Jihar Fulato, sai cibiyar ta dakatar da taimakon da take bayarwa baki dayansa.

“Manoman Kano na kan gaba a wadanda hakan ta fi shafa wanda kuma hakan ya shafi noman da ake yi na alkama,” in ji shi.

Shi ma wani manomin a Jihar Kanon mai suna Malam Habibu Hassan cewa ya yi, an mayar da noman alkama koma baya, duk da matukar bukatar alkmar da ake yi don amfanin cikin gida.

Sai kuma ya yi kira ga gwamnati da ta ba noman na allkama kulawar da ta ba wa Shinkafa, wanda hakan zai sa a noma ta a gida yadda ya kamata. La’akari da yadda karancin alkamar ya damu kowa, sakamakon yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukiraine.

Ya kuma ce, yakin na kasashen biyu kamata ya yi ya zama kaimi ga matasan kasar nan, su rungumi noman ka’in-da-na’in.

Manomin ya kuma koka kan yadda manoman alkama suke komawa noman Shinkafa saboda kulawar da kuma tagomashin da noman shinkafar yake samu.

“Mun dauka cewa gwamnati za ta karfafe mu ta hanyoyin da take da su na shiga noman damina.

“Amma abin mamaki sai ga shi hatta noman ranin da muke yi don na alkamar ma ya faskara, ganin yadda a yi watsi da mu.

“Domin babu wani abin tallafi da muke samu daga gwammnti, ta nade hannu kawai ta kyale mu.

“Gaskiya idan aka ci gaba a haka, babu shakka manoma da yawa za su yi watsi da noman,” inji shi.

Wani abin mamaki shi ne wadannan korafe-korafe na zuwa ne a daidai lokacin da Ministan Kula da Harkokin Noma da kuma Wadata kasa da abinci, Sanata Abubakar Kyari yake ikirarin cewa, ba zai taba lamintar zunzurutu Dala Biliyan Biyu da ake kashewa wajen shigo da alkama kasar nan ba a duk shekara.

Sai dai duk da cewa Ministan ya fito karara ya bayyana cewa, Nijeriya na da duk albarkatun da ake da bukata na zama mai dogaro da kai ta fuskar wadata kasa da alkama, sai dai babu wani abin a-zo-a-gani gani da ta yi na taimaka wa manoma a jihohin da ake noman alkamar.

Idan za a iya tunawa a wani rahoto da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar a 2020 ya nuna cewa, Nijeriya na da filin noman da girmansa ya fi hekta Miliyan daya da za a iya nomawa.

Sai dai kamar yadda masu magana ke cewa, “ana kukan targade sai ga karaya ta faru”. Ma’ana, ana batun wadatar filin noma, manoman alkama na kukan rashin ba su kulawa duk da cewa lokacin shukarsu ya kusa.

Sai dai wani bincike ya nuna cewa,wasu kamfanonin samar da irin shuka da kuma masu injinin Casa a kasar nan, sun dauki gabarin samar da ingantaccen irin shuka ga manoma domin shukawa.

A cewar Malam Sani Aliyu, wani manomin alkama, wasu Kamfanonin suna rarraba irin shuka ga manoma domin fara shuka a gonakinsu.

Hakan, inji shi, ba zai taimaka wa noman alkama ba duk da cewa “Da babu”, inji masu iya magana, “gwara ba dadi”.

“Tuni dai wasu kamfanonin samar da irin shuka suka soma rarraba irin shuka ga wasu amintattun manoma domin shukawa.

Kuma irin shukar da suke rarraba sun fi sauran da muke amfani da su samar da amfani da kimanin kashi 25.

Sai dai tambayar a nan ita ce, ta yaya haka zai bunkasa noman alkama a kasar? Babu shakka masu irin za su samu fa’ida.

“To amma manoman su nawa ne kuma wanne irin bunkasa ko habaka za a samu daga ‘yan kalilan? Wadannan su ne abubuwan duba wa,” in ji shi.

Ya kuma ce, abin takaici ne kawo yanzu da aka soma shirye-shiryen shuka alklama babu wani abin da gwamnati ta yi ta fuskar taimaka wa manoma.

Yana mai cewa, kamata ya yi mu soma ganin wani abu a kasa.

“Masu nika ne da kuma injinan casa su suke yin wani abu a yanzun nan.

“Lokaci dai tafiya yake yi kuma duk wani abin da ba a yi shi a yanzu ba, a lokacin da ya kamata, nan gaba idan an yi shi ma barna ce da kuma bata lokaci.”

Koyaushe gwamnantin za ta dauki matakin da ya dace wajen noman alkama da wadatar da shi a kasar nan. Mun dai zura ido muna kuma jira.

%d bloggers like this: