✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta bayar da ratar fiye da kuri’u dubu 200 a Zaɓen Gwamnan Kogi

Sakamakon zaben kananan hukumomi uku kacal ne suka rage a yayin da INEC ta dage zaman tattara sakamakon.

Jam’iyyar APC ce ke kan gaba da gagarumin rinjaye a sakamakon zaɓen kananan hukumomi 18 na Jihar Kogi wanda Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta bayyana kawo yanzu.

Usman Ododo, dan takarar jam’iyyar mai mulki, ya samu nasara a kananan hukumomi 11, sai Muri Ajaka na jam’iyyar SDP da ya samu nasara a kananan hukumomi shida, yayin da kuma Leke Abejide na jam’iyyar ADC ya samu a karamar hukumar daya.

Ya zuwa yanzu dai, Ododo ya samu kuri’u 409,450, Ajaka kuwa ya samu 208,503 yayin da Dino Melaye na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 41,925 kacal.

INEC ta dage zaman tattara ragowar sakamakon zaben na kananan hukumomin Kogi uku da suka yi saura.

Ga dai sakamakon zaben kananan hukumomin da INEC ta fitar kawo yanzu:

Okehi

APC 53,0623
PDP: 2,722
SDP: 153

Yagba East

APC: 7,096
PDP: 2,615
SDP: 312

Ijumu

APC 10,524
PDP: 6,909
SDP: 356

Mopa-Muro

APC: 5,077
PDP: 1,562
SDP: 253

Adavi

APC: 101,156
PDP: 1,005
SDP: 268

Ofu

APC: 5,245
PDP: 293
SDP: 28,768

Koton Karfe

APC: 14,769
PDP: 2,974
SDP: 8,441

Bassa

APC: 9,519
PDP: 3,605
SDP: 7,543

OmalaSakamamkon zabe 

APC: 2,902
PDP: 832
SDP: 18,160

Olamaboro

APC: 5,572
PDP: 1,376
SDP: 22,173

Ankpa

APC: 8,707
PDP: 3,654
SDP: 43,258

Okene

APC: 138,416
PDP: 1,463
SDP: 271

Dekina

APC: 9,174
PDP: 499

SDP: 47,480

Ajaokuta

APC: 23,211
PDP: 483
SDP: 8,869