Wasu masu zanga-zanga sun yi dafifi a hedikwatar Jam’iyyar APC mai mulki da ke Abuja, suna neman shugabanta na kasa, Abdullahi Ganduje, ya sauka daga mukaminsa.
Masu zanga-zangar suna kuma kira ga Shugaba Bola Tinubu da Sakataren Gwamnati, George Akume, su duba yiwuwar mayar da shugabancin jam’iyyar yankin Arewa ta Tsakiya.
Suna neman Ganduje ya sauka ne kwanaki biyu bayan shugabannin APC na jihohi sun jaddaga goyon bayansu da amincewa ga shugabancinsa.
Shugabannin jam’iyyar daga jihohin da ke fadin Najeriya sun sanar da goyon bayansu ga Ganduje ne a lokacin ziyarar aiki da suka kai masa a ofishinsa.
Daga cikin masu zanga-zangar, akwai masu dauke da kwalaye da ke dauke da rubutun neman murabus din Ganduje, da masu neman shugabancin jam’iyyar ya koma yankin Arewa a Tsakiya idan ya sauka.
Suna wannan kiraye-kiraye ne bayan dambarwar dakatar da Ganduje da wani tsahin shugabannin mazabarsa da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da shi.
Sun sanar da dakatar da shi ne kan zargin da almundahar kudade da cin rashawa a lokacin da yake gwamnan jihar da giwamnatin jihar mai ce ke masa.
Sai dai daga bisani wani tsagin shugabanincin mazabar ya yi wasi da su, lamarin da ya kai su kotu kuma kotu a amince da dakartarwar.
Amma daga bisani kotun ta janye dakarawar, sai da kuma har yanzu kurarar ba a gama lafawa ba.