✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

INEC ta ba da umarnin sake gudanar da zabe a Kogi

Za a sake gudanar da sabon zabe a yankunan da lamarin bayyana sakamakon zabe na bogi ya shafa.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayar da umarnin sake gudanar da zabe a wasu gundumomi na Jihar Kogi sakamakon abin da ta kira kura-kurai da suka saba wa ka’ida.

Jihar Kogi dai na daya daga cikin jihohi uku da aka gudanar da zabuka gwamna a ranar Asabar.

Biyo bayan wasu takardun sakamakon zabe na bogi wadanda suka yadu a yayin da ake ci gaba da kada kuri’a tun a jiya Asabar, INEC ta sanar da dakatar da zabukan a gundomomi tara sannan ta ce za sanar da matakin da za ta dauka kan lamarin.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Mohammed Haruna, kwamishinan bayanai da wayar da kan masu zabe na INEC, ya ce za a sake gudanar da sabon zabe a yankunan da lamarin ya shafa “kamar yadda tun a jiya na yi alkawarin za a dauki matakin da ya dace.”

Aminiya ta ruwaito cewa, ana tsakar zaben ne wata kungiyar kare hakkin bilAdama ta Yiaga Africa ta kwarmata yadda aka soma fitar da takardun sakamakon zabe na bogi a jihar ta Kogi.

Nan da nan dai INEC ta tari hanzarin lamarin inda ta ce ta tsunduma cikin bincike.

Kan haka ne Mohammed Haruna ya ce INEC ba za ta karbi sakamakon zaben da ake ikirarin an fitar da na bogi ba daga rumfunan zaben da abin ya shafa.

Haruna ya ce wannan lamari na fitar da sakamakon zabe na bogi ya auku ne a kananan hukumomin Adavi, Ajaokuta, Ogori/Magongo, Okehi da kuma Okene.

A cewarsa, lamarin ya fi muni a Karamar Hukumar Ogori/Magongo, inda ya shafi rumfunan zabe 9 daga cikin goma da ke yankin.

“Saboda haka ba za mu karbi duk wani sakamakon zabe da ya fito daga wadannan kananan hukumomi ba.

“Mun dakatar da zabe a wasu unguwanni 9 da ke Karamar Hukumar Ogori/Magongo da suka hada da Eni, Okibo, Okesi, Ileteju, Aiyeromi, Ugugu, Obinoyin, Obatgben da Oturu.

“Sauran wuraren da irin wannan aika-aikar ta shafa a ragowar kananan hukumomin muna ci gaba da gudanar da bincike a kansu, kuma nan da awa 24 za mu sanar da matakin da muka dauka a kai.

“Muna da bayanan duk wasu ma’aikatanmu da suka hada da masu lura da sanya ido a kan ayyukan zabe, kuma duk wanda muka samu da laifi za a dauki matakan da suka dace a kansu.”