Kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF) da takwararta ta Dattawan Arewa (NEF) da wasu kungiyoyin matasan Arewa 16 sun yi Allah wadai da yunkurin mayar da wasu ofishoshin Babban Bankin Nijeriya (CBN) da na Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama (FAAN) daga Abuja zuwa Legas.
Kungiyar ACF a sanarwar da ta fitar dauke da sa hannun Kakakinta Farfesa Tukur Muhammad-Baba ta bayyana yunkurin a matsayin wanda zai cutar da Arewa.
- Yadda muka fanso ’yan uwan Nabeeha daga masu garkuwa —Dangi
- Yadda Katsinawa suka koma sufuri da shanu da jakuna da kekuna
A ranar 13 ga Janairu Bankin CBN ya sanar da cewa yana shirin mayar da wasu ofishoshista zuwa Legas don ta rage cinkoso a hedikwatarsa a Abuja.
A cewar Bankin, matakin ya yi daidai da dokar kula da lafiyar gidaje da kuma samar da yanayin aiki mai kyau.
Kwana biyu bayan CBN ya fito da tasa sanarwar Ministan Sufurin Jiragen Sama Festus Keyamo a wata wasika ranar 15 Janairu, wadda Janar Manajan Hukumar FAAN, Olubunmu Kuku ya sa wa hannu ya ba da umurnin dauke hedikwatar hukumar zuwa Legas daga Abuja.
Sai dai bayan taron ACF da Sanata Aliyu Magatakarda Wamako a ranar Lahadi ta nuna adawarta da yunkurin mayar da manyan hukumomin Gwamnatin Tarayyar biyu zuwa Legas.
Ita ma Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) a ranar Juma’a ta nuna rashin amincewa da wannan shiri wanda ta ce zai kara fadada gibin tattalin arzikin a tsakanin Arewa da Kudu.
ACF ta ce duk da za a iya kawar da fuskar daga wannan yunkuri na CBN da FAAN sai dai zai yi wuya a gaza zargin cewa yunkuri ne don dannewa ko nuna bambanci ga Arewa.
Ta ce matakin na CBN da FAAN abin damuwa ne da wasu hukumomin Gwamnatin Tarayya ke yi don kuntata wa Arewa.
“Daga sanarwar CBN, sai ga sanarwar Hukumar FAAN na komawa Legas saboda wai karancin ofisoshi da wai yawan jiragen da ke sauka a Legas.
“Wannan shiri na hukumomin biyu wasu dabaru ne kawai. Kuma cikin daraktoci 40 da aka nada kwanan nan a Hukumar FAAN su ma hudu ne kawai ’yan Arewa,” in ji ACF.
ACF ta ce Arewa ta dade tana fuskantar barazana da matsaloli irin wadannan. Ta ce sararawar da kawai aka samu ita ce ta samun man fetur a Arewa a Kogin Kolmani wanda ya rage farfagandar da ake a kan Arewa.
Kungiyar ta ba ta gamsu da hujjojin da aka bayar kan yunkurin mayar da hukumomi biyu zuwa Legas ba.
Sai ta bukaci Gwamnatin Tarayya da Majalisar Dokoki ta Kasa su haana wannan yunkuri tare da fito da hanyoyin da za su magance cinkoson da ake zargin ana fama da shi a Abuja.
“Akwai filaye da yawa a Abuja da za a iya amfani da su wajen fadada ginin kowace hukuma. Don haka kada a yi amfani da wannan hujja wajen cim ma wata boyayayyar manufa,” inji ACF.
Su ma kungiyoyin matasan Arewa 16 a wata takardar bayan taro da suka gudanar a Gidan Arewa da suka aiko wa Aminiya a ranar Laraba dauke sa hannun shugaban taron Murtala Abubakar da Babban Jami’in Watsa Labarai Hashim Tom Maiyashi da kuma Babbar Jami’ar Tuntubar Mata, Latifa Abdussalam sun ce kungiyoyin matasan Arewa suna Allah wadai da wannan yunkuri.
A cewarsu, hukumomin biyu ba su da wata hujja ta mayar da ofisoshin nasu biyu zuwa Legas. Kuma hakan zai jawo matsalolin rayuwa da raunana hadin kan kasa, kuma hakan ya saba wa dokar tabbatar da Abuja a matsayin hedikwatar kasa.