✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Katsinawa suka koma sufuri da shanu da jakuna da kekuna

Halin da ake ciki a yanzu yana da ban-tausayi, yana jefa mutane cikin wahala, yunwa a ko’ina.

A tsakiyar tsadar rayuwa wadda ta biyo bayan cire tallafin man fetur, wasu mazauna birnin Katsina da wasu yankunan jihar sun koma amfani da tsofaffin hanyoyin sufurin kayayyaki da mutane.

Mazaunan sassan birnin wadanda galibi masu karamin karfi ne, sun yanke shawarar rage nauyi da kuncin rayuwa da halin kaka-ni-ka-yi da suka samu kansu a ciki ne don kaurace wa shiga wani mawuyacin hali a lokacin rashin tabbas da tattalin arziki ke fuskanta.

Yanzu haka dai da dama mazauna Katsina suna amfani da kekunan shanu da jakuna da kuma kekuna wajen jigilar kayayyaki daga wannan wuri zuwa wancan saboda tsadar abin hawan da ya dogara da man fetur wanda ke dada tsada a yanzu.

A yanzu mutanen suna amfani da keken shanu wajen kai kayan amarya (kayan daki) gidan miji a cikin birni saboda hayar babbar mota ko motar daukar kaya na da tsada duk da saurin da take da ita, in ji Nuraddeen Isma’il da ke tuka keken shanu.

“Mutane suna son rage farashin ne tare da rage nauyin shiga manyan motoci wajen kai kayan daki gidan amarya.

“Lokacin da ake gudanar da bukukuwan aure na jama’a, muna samun kusan Naira dubu 20,000 ko 30,000 a kullum ta hanyar karbar Naira 7,000 ko N10,000 a kowace tafiya, don jigilar kayan amarya, ya danganta da wurin ko iyawar wanda abin ya shafa wanda yawancin masu karamin karfi ne a yanzu.

“Muna jigilar kayayyakinsu da wasu jama’arsu zuwa wurare daban-daban a birnin Katsina da kewaye saboda ba su da kudin da za su iya sayen mai ga motocinsu ko ba su da motocin da za su yi musu aikin,” in ji Isma’il.

Tun cire tallafin man fetur da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya yi a watan Mayun bara, kasuwanci ya daina zama kamar yadda al’ummar Katsina suka saba, don haka aka yanke shawarar tsara hanyoyin shawo kan lamarin.

Hakazalika, mutane irin su Fahad Abdullahi na amfani da jakunansa wajen kai yashi da sauran kayan gini kamar siminti da tubali zuwa wuraren gini a Katsina kan kudi kalilan ga masu karamin karfi, wadanda ba za su iya daukar tifa ba wadanda galibi suna karbar makudan kudi bayan cire tallafin man fetur.

“Wannan wata dama ce a gare mu yayin da a yanzu muke samun kudi a kullum daga wannan sana’a wadda a da take daf da bacewa.

“A da, muna kai kowane buhun yashi a kan Naira 50 amma a yanzu muna karbar Naira 200 kuma ina iya yin sawu 50 a rana ta amfani da jakunana guda shida. Don haka, mun yi amfani da damar cire tallafin man fetur don yin rayuwa kuma wannan ita ce rayuwa a gare mu.

“Mun sha wahala sosai a baya lokacin da yawancin mutane ke amfani da manyan motoci ko tifa don kai yashi da sauran kayan gini, da kyar nake samun Naira 1,000 a rana amma wannan mawuyacin lokaci ya wuce,” in ji Abdullahi.

Bayan cire tallafin mai wanda ya haifar da hauhawar farashin kaya, farashin jakuna a kasuwa ma ya tashi a cewar Fahad Abdullahi.

Sai dai ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu ya bullo da shirye-shiryen da za su magance wahalhalun da ’yan Nijeriya suke fuskanta a kullum.

A yanzu, wasu ma’aikatan gwamnati a Katsina kamar Halliru, Nuhu da Habibu Musa da ke amfani da babura suna zuwa wuraren aikinsu sun yi watsi da su, yanzu haka suna amfani da keke saboda ba sa iya sayen mai.

“Daga gidana zuwa wurin aikina kusan kilomita 12 ne, kuma ina kashe akalla Naira 1,000 don yin amfani da babur a kullum don in je in dawo. A ina zan samu kudin da zan ci gaba da yin haka alhalin ba a kara komai a albashina na wata-wata a yanzu ba? Hatta ma’aikatan jinya da gwamnati ke ta surutu a kai, ba mu ga komai ba har zuwa yanzu.

“Ina so ku shaida wa duniya cewa masu karamin karfi wadanda su ne mafi yawan ’yan Nijeriya suna shan wahala kuma suna cikin mawuyacin hali,” in ji Halliru Nuhu.

Masu sharhi a kan al’amurran yau da kullum a Katsina, kamar Dokta Bashir Usman Ruwan Godiya yana ganin cewa tabarbarewar tattalin arzikin kasa na bukatar haɗa ƙarfi da ƙarfe da gwamnati don magance matsalolin.

“Kowane sashe na tattalin arzikin Nijeriya ya tabarbare kuma lamarin na ci gaba da tsananta yayin da wahala ke kara ta’azzara kowace rana.

“Misali dubi masu sana’a da kananan ’yan kasuwa a ko’ina, kaso mafi yawa daga cikinsu sun durkushe ko suna fafutikar rayuwa. Mutane da yawa sun shiga wahala ba tare da samun wata hanyar rayuwa ba.

“Halin da ake ciki a yanzu yana da ban-tausayi, yana jefa mutane cikin wahala, yunwa a ko’ina, ga hauhawar farashin kayan rayuwa, na jefa mutane da yawa a cikin wahala,” in ji shi.

Ruwan Godiya ya ce, da tun farko gwamnati da sauran masu ruwa-da-tsaki su yi wani abu don shawo kan lamarin, wanda zai kyautata wa Nijeriya a matsayinta na kasa. ’

’Yan Nijeriya da dama sun tsara wasu hanyoyin da za su bi don shawo kan lamarin, kamar yadda Hukumar Kididdiga ta Kasa ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki ya kai kashi 28.92 a baya-bayan nan.

Yayin da wasu ke fafutikar samun abin da za su ci don a dunkule jiki da ruhi, wasu kuma na amfani da wasu hanyoyin sufurin da za su tanadi kudi don wasu muhimman bukatu kamar kudin makaranta, matsuguni, kula da lafiya da sauran wasu bukatu na yau da kullum.