✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gidauniya ta yi wa masu cutar gwaiwa dubu 12 tiyata kyauta a Katsina

Gidauniyar ta kuma bayar da maganin ido da tiyata kyauta ga marasa lafiyar idon a jihar.

Gidauniyar attajirin ɗan kasuwar nan na Jihar Katsina, Alhaji Dahiru Mangal, ta yi wa masu fama da cutar gwaiwa da taruwar ruwa a wasu sassan jiki fiye da 12,300 tiyata kyauta.

Da yake yi wa wakilin bayani, Malam Husaaini Kabir, mamba a kwamitin amintattu na gidauniyar ne ya tabbatar da hakan a Katsina, a lokacin ƙaddamar da aikin kashi na biyu.

Kabir ya bayyana cewa gidauniyar tana gudanar da aikin tiyatar da bayar da magani kyauta a duk bayan watanni uku tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 2013.

Ya ƙara da cewa, “majinyata masu rauni tsakanin 500 zuwa 600 ne ke cin gajiyar aikin tiyatar gwaiwar da na rage ruwan kyauta a jihar.

“Wannan shiri ba wai yana taimaka wa mutanen garin Katsina ne kawai ba, yana kuma tallafa wa mazauna ƙauyukan jihar da kuma yankunan da ke makwabtaka da su.

“Manufarmu ita ce rage nauyin biyan kuɗin kiwon lafiya ga mutane masu ƙaramin ƙarfi waɗanda ke gwagwarmaya don biyan buƙatun yau da kullun,” in ji shi.

Kabir ya buƙaci sauran ƙungiyoyi da masu hannu da shuni da su tallafawa irin wannan shiri, musamman don taimaka wa ƙoƙarin gwamnati a fannin kiwon lafiya.

Ya jaddada mahimmancin aikin tare don tunkarar ƙalubalen kiwon lafiya a cikin al’ummomin da ba a yi musu hidima ba.

Wasu da suka ci gajiyar shirin sun yaba da shirin tare da ƙarfafa gwiwar gwamnati, ƙungiyoyi masu zaman kansu, da masu hannu da shuni da su yi koyi da hakan.

Sun bayyana cewa sun jure yanayin da suke ciki na tsawon shekaru amma ba za su iya yin tiyatar ba saboda matsalar tattalin arziki.

Aminiya ta ruwaito cewa gidauniyar ta kuma bayar da maganin ido da tiyata kyauta ga marasa lafiyar idon a jihar.