✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Kadiriya sun yi taro kan cin zarafin Almajirai a Gombe

Makarantun tsangayu da na Islamiyya 150 ne suka halarci taron daga cikin garin Gombe.

Mabiya Darikar Kadiriya a Jihar Gombe sun gudanar da taro kan yadda a shekarun baya bayan nan ake samun malamai da cin zarafin Almajarai a tsangayu.

Shugaban Darikar Kadiriyar a jihar, Sheikh Muhammad Muhammadu Basakkwace, ya ce an shirya taron ne laakari da yadda aka bar su a baya ba sa tafiya tare da zamani.

Ya ce azabatar da Almajirai da wasu malamai ke yi da har ta kai ga lauyoyi da hukumomin kare hakkin dan Adam sun shiga lamarin ba daidai bane.

Sheikh Muhammad Basakkwace, ya bayyana cewa yawaitar faruwar cin zarafin ya sa suka shirya taron, inda suka gayyato masana da masu ruwa da tsaki domin su wayar musu da kai.

A cewarsa, taron ya taka muhimmiyar rawar gani ta yadda Malamai da dama sun koma da farin ciki da gamsuwa da suka yi wajen sanin yadda za su zauna da Almajiran su.

Wani lauya da ya gabatar da Kasida a wajen taron, Barista Hassan Umar, ya ce a tsarin koyarwa akwai nau’in horo da ya kamata a yi wa dalibi wanda bai wuce ka’ida ba amma ba azabatarwar da za ta kai ga har Yaro ya rasa wani sashin na jikinsa ba.

Da yake yi wa Aminiya karin bayani, lauyan ya ce bai wa Yaro horo daidai gwargwado da zai sa ya ji tsoro ya fi a azabatar da shi.

Ya kara da cewa, muddin aka yi wa yaro horon da bai wuce kima ba, da zarar ya tuna da wannan horon zai kiyaye aikata laifi a gaba.

Wasu daga cikin malaman Islamiyya da Aminiya ta zanta da su sun bayyana gamsuwa kan yadda taron ya gudana, suna mai cewa babu shakka sun gane akwai hukuncin da ke wuce gona da iri da malaman ke yi wa Almajirai.

Sun bayyana cewa sun gane ko a babin hankalin akwai hukuncin da ba a yarda malami ya yi ba balle a yi ta dukan Yaro ko mummunan dauri da zai yi masa illa.

Makarantun tsangayu da na Islamiyya 150 ne suka halarci taron daga cikin garin Gombe.

Wasu daga cikin malaman da suka zanta da Aminiya sun hada da Sa’idu Abubakar Mai Ashafa daga Darul Huda Littahafizul da ke Qur’an Unguwar Federal Low cost da Malama Aishatu Abubakar daga Unguwar Tudun Wada Layin Shamaki,