Gwamnatin Jihar Kano, ta kudiri aniyar gina sabbin makarantun sakandare 120 don cike gibin makarantun da ake da su a jihar.
Gwamnatin Jihar ta ce fiye da dalibai 23,000 ne suka daina zuwa makaranta sakamakon rufe makarantun kwana 28 da gwamnatin Ganduje ta yi a baya.
- An shiga rudani bayan bacewar Murja daga gidan yari a Kano
- ’Yan bindiga sun kone mutum 12 da ransu a Kaduna
Kwamishinan Ilimin jihar, Dokta Umar Haruna Doguwa ne, ya bayyana haka a lokacin taron wayar da kan iyaye kan muhimmancin ilimin mata da kuma bunkasar tattalin arzikinsu a jihar.
Doguwa ya kara da cewa a yanzu haka gwamnatin jihar na kokarin bude makarantun kwanan da Ganduje ya rufe, domin dawo da daliban kan tafarkin karatunsu.
“A yanzu gwamnati ta kuduri aniyar samar da makarantun sakandire sama da 120 a fadin jihar don cike gibin rashin isassun makarantu a fadin jihar nan.”
Doguwa, ya bayyana cewa iyaye musamman mata suna da rawar takawa wajen ganin ‘ya’yansu sun samu nagartaccen ilimi.
“Sanin muhimmancin da iyaye mata ke da shi a rayuwar ‘ya’yansu ya sa muka kira su don wayar musu da kai a kan muhimmancin ilimin ‘ya’yansu.
“Gwamnatin tana iya kokarinta wajen ganin ta samar da kayayyakin aiki a makarantu, abin da ya rage shi ne iyaye su sauke nasu nauyin wajen yin abin da ya kamata don ganin ‘ya’yansu sun je makaranta a kan lokaci tare da bibiyar karatun ‘ya’yansu.”
Ita ma a nata jawabin, Kwamishiniyar Al’amuran Mata ta Jihar Kano, Aisha Lawan Saji, ta bayyana cewa mata su ne kashin bayan ci gaban kowacce al’umma, don haka dole ne su karfafa ‘ya’yansu musamman mata wajen neman ilimi don su zama al’umma ta gari.
“Sai mace ta yi ilimi za ta iya tallafa wa ‘ya’yanta ta hanyar bibiyar karatunsu da kuma sauran al’amura da suka shafi rayuwarsu.
“A wannan lokaci da ake amfani da kafar sada zumunta idan har ba ki da ilimi ta yaya za ki san irin hatsarin da ke cikin wannan lamarin ballantana ki dauki matakin hana faruwar wasu abubuwa duba da cewa irin wadannan abubuwa ana sanya su ne a harshen Turanci.”
Ita ma a nata bangaren, Mataimakiyar Babbar Kwamanda a bangaren Mata, Dokta Khadija Sagir Sulaiman, kira ta yi ga iyaye mata da su dage wajen kula da tarbiyyar ‘ya’yansu don ganin sun zama nagartatttu kuma abun alfahari.
“Babu shakka ilimi shi ne gishirin zaman duniya dole ne sai iyaye mata sun ja ‘ya’yansu jikinsu tare da yi musu tarbiyya don su zama nagartattun iyaye wadanda al’umma za ta yi alfahari da su a nan gaba.”