✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kone mutum 12 da ransu a Kaduna

Maharan sun kone mutanen da ransu.

’Yan bindiga sun kone mutum 12 da ransu a kauyen Gindin Dutse Makyali, Doka da ke gundumar Kufana, a Karamar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna.

Maharan sun kuma kone gidaje 17 a kauyen yayin farmakin da suka kai da misalin karfe 6:00 na safiyar ranar Lahadi.

Wani mazaunin yankin, Mista Stephen Maikori, ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin, inda ya ce maharan sun jikkata wasu mutum bakwai.

“Da safiyar yau (Lahadi) 18 ga watan Fabrairu, 2024 da misalin karfe 6:00 na safe ‘yan bindiga sun kone mutum 12 da ransu, sannan sun jikkata wasu bakwai yayin harin.

“Bugu da kari, sun koe gidaje 17 a kauyen,” in ji shi.

Aminiya ta ruwaito yadda maharan suka bude wa wasu mutanen kauyen wuta, sannan suka yi awon gaba da wani mutum guda daya.

Jihar Kaduna dai na ci gaba da fuskantar kazaman hare-haren ’yan bindiga, lamarin da ya yi sanadin salwantar rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

Gwamnan jihar, Uba Sani ya jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a harin, sannan ya yi Allah-wadai da harin da ‘yan bindigar suka kai yankin.

Gwamnan ya kuma umarci Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) da ta tallafa wa iyalan wadanda harin ya rutsa da su.

Gwamnan ya kara jaddada aniyarsa na magance matsalar tsaro da jihar ke fuskanta.