✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum 9, sun sace tsohon daraktan CBN a Kaduna

Maharan sun sace mutane 35 a yankunan biyu.

Akalla mutum tara ne ‘yan bindiga suka kashe a yankin Kwasam da ke Karamar Hukumar Kauru da kuma unguwar Gwada da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

’Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da mutum 35, ciki har da tsohon Daraktan Babban Bankin Najeriya (CBN), Zakariya Markus.

Kazalika, maharan sun jikkata mutum tara a harin da suka kai a kananan hukumomin biyu.

A cewar wasu majiyoyi, lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da misalin karfe 10 na dare lokacin da ‘yan bindigar suka mamaye yankin.

Wata majiya ta ce ‘yan bindigar sun tilastawa wasu mutum biyu nuna gidan tsohon ma’aikacin na CBN, kafin daga bisani suka sace shi tare da wasu.

“’Yan bindigar sun koma gidan, sannan suka yi awon gaba da dan uwansa da matar dan uwan.

“Mazauna yankin sun yi yunkurin kubutar da mutanen da suka sace, amma ‘yan bindigar suka bude musu wuta tare da kashe mutum shida nan take.

“Nan take suka yi awon gaba da wadanda suka sace a yankin.”