✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An Kashe Sakataren Yada Labaran APC Na Filato 

Mahara sun harbe Sakataren Yada Labaran Jam’iyyar APC na Jihar Filato, Sylvanus Namang, har lahira

Wasu da ba a san ko su wane ne ba sun harbe Sakataren Yada Labaran Jam’iyyar APC na Jihar Filato, Sylvanus Namang, har lahira a Karamar Hukumar Pankshin da ke jihar.

Wani jigo a jam’iyyar da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa Namang ya rasu ne sakamakon raunukan da ya samu a harin da aka kai masa a garin Pankshin.

An kashe Namang ne a wajen dakin otal dinsa da ke yankin inda ’yan bindigar suka bude masa wuta da misalin karfe 7:30 na safe ranar Asabar.

Majiyar ta shaida wa Aminiya cewa marigayin ya bar gida ne a ranar domin halartar jana’izar da aka yi a Pankshin inda ya gamu da ajalinsa.

Ya kara da cewa Marigayi Namang ya kasance amintaccen mutum mai kishin ci gaban APC a dukkan matakai.

A cewarsa, jam’iyyar na shirin bayar da sanarwa dangane mutuwar.