✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar kwastam ta yi gwanjon motoci 462

Ana zargin hukumar kwastam da karkatar da motoci 300, a yayin da take shirin yin gwanjon wasu kusan 500

Ana zargin Hukumar Kwastam ta Najeriya da jami’anta sun karkatar da motoci 300, a yayin da take shirin yin gwanjon wasu motoci kusan 500.

Zargin na zuwa ne bayan hukumar kwastam ta sanar da fara gwanjon motoci 462 da ta kama a hannun masu laifi, wadanda darajarsu ta kai Naira miliyan 556.7.

Kakakin hukumar kwastam, Abdullahi Maiwada, ya ce tuni hukumar ta sanya hotunan motoci 476 a shafinta, domin masu sha’awa su zaba.

Kimanin mutane 14,000 ne suka tura bukatarsu ta sayen motocin ta shafin hukumar kwastam din na intanet.

Sai dai kuma ’yan kasuwa masu shige da ficen motoci sun yi zargin cewa hukumar da ma’aikatanta sun karkatar da wasu motoci 300.

Shugaban kungiyar dillalan motoci (NAGAFF), Alhaji Tanko Ibrahim, ya zargi hukumar da wasa da hankalin jama’a da kuma zalunci.