✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta kama motoci 21 maƙare da kayan abinci a hanyar fita ƙetare

An kama kayan abincin da ake shirin kaiwa N’djamena Jamhuriyyar Chadi, da Jamhuriyyar Afirka ta Tsakiya da Kamaru.

Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arziki Ta’annati EFCC ta kama wasu motocin dakon kaya 21 maƙare da kayan abinci da wasu kayayyaki da ke kan hanyar N’djamena a Jamhuriyyar Chadi da Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka da Kamaru.

Jami’an na EFCC sun kama manyan motocin ne yayin wani samame da aka ƙaddamar kan titunan Kalabiri/Gamboru Ngala da Bama a Jihar Borno.

Binciken da aka gudanar ya nuna wasu kayan abinci da aka yi dabarar ɓoye su cikin motocin da za su iya wucewa ba tare da an gano ba.

Ƙarin binciken da aka gudanar ya nuna takardar da aka nannaɗe kayan da ke cikin motar ta nuna kayan za a kai su N’djamena a Kasar Chadi da Jamhuriyyar Afirka ta Tsakiya da kuma Kamaru.

Ana sa ran kamen motocin zai kawo ƙarshen matsalar abincin da ake fama da shi sakamakon yadda wasu ke fasaƙwabrinsa.

Wakilinmu ya ruwaito cewa ana gudanar da bincike kan mutanen da ake zargi kuma za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.