Hukumar Tara Kudaden Haraji ta Jihar Kaduna (KADRIS) ta raufe rassan bankin UBA kan kin biyan harajin Naira miliyan 14.
KADRIS ta rufe rassan bankin guda shida da ke Kaduna ne bayan hukumar gudanarwar bankin ya gaza biyan harajin da ake bin su, duk da takardun tunatarwar da hukumar aike musu a lokuta daban-daban.
Sakataren Majisar Gudanarwar kusa Mai ba da Shawara kan Shari’a ta KADRIS, Barista Aysha Muhammad da rakiyar jami’an tsaro ta jagoranci rufe rassan bankin.
A cewarta, hukumar ta dauki matakin ne da nufin karbo bashin kudaden haraji Naira N14,367,322.20k da suke bin bankin daga shekarar 2019 zuwa 2021, kamar yadda dokar hukumar ta tanadar.