✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tinubu na amfani da talauci a matsayin makami — Atiku

Rotimi Amaechi ya danganta ƙaruwar rashin tsaro a ƙasar da yawaitar talau

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, da yin “amfani da talauci a matsayin makami” domin juya ’yan Najeriya.

Da yake jawabi a Abuja ranar Asabar a wajen lacca na cika shekaru 60 da haihuwar tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, mai taken “Amfani da Talauci a Najeriya,” Atiku ya yi zargin cewa gwamnati tana amfani da matsalar tattalin arziki don sarrafa ’yan kasa.

Ya ce, “Abin da muke fuskanta a halin yanzu a Najeriya shi ne gwamnati tana amfani da talauci a matsayin makami.”

Atiku ya yi nuni da bambancin yanayin rayuwa a yanzu da lokacin ƙuruciyarsa, inda ya  ce a lokacin Kano tana cikin yalwar arziki, ba a saba ganin mutane marasa matsuguni ba.

A cewarsa, yanzu lamarin ya canza, ta yadda talauci da rashin tsaro sun kai ga mutane suna barci a kan tituna da kuma karkashin gadoji a cikin birni Kano.

Har ma ya yi iƙirarin cewa an umarci wata hukumar jihar Kano da aka ɗora wa alhakin taimaka wa waɗannan mutane da ta dakatar da ayyukanta.

Atiku ya bayyana shigarsa cikin wata ‘gamayya siyasa’ don yaƙar wannan yanayi, yana mai cewa, “muna cikin wannan haɗin gwiwa don tabbatar da cewa ba za mu bari su ci gaba da amfani da talauci a matsayin makami ba.”

Da yake mai da martani ga kalaman Atiku, Rotimi Amaechi ya danganta ƙaruwar rashin tsaro a ƙasar da yawaitar talauci.

“Yunwa ba ta san ƙabila da addini ba, kuma gwamnatin yanzu ta sa mutane sun ƙara talaucewa, wanda hakan ya ƙara yawan rashin tsaro da aikata laifuka,” in ji Amaechi.

Tsohon ministan sufurin ya tunatar da ’yan Najeriya cewa ikon ƙarshe yana hannunsu, yana mai kira gare su da su yi amfani da damarsu ta kaɗa ƙuri’a don tumbuke shugabanni idan ba su gamsu ba.