Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin dawo da shirin Gwamnatin Tarayya na ciyar da dalibai a makarantu.
Tinubu ya dawo da shirin ciyar da daliban ne da nufin rage yawan kananan yara marasa zuwa makaranta da suka gararamba a kan tituna.
Gwamnatin da ta gabace shi, ta tsohon shguaban kasa Muhammadu Buhari ce ta dakatar da tsarin bayan shekaru da farawa.
Amma Tinubu ya ce dawo da tsarin zarin samar da mafita daga matsalar rashin zuwa makaranta a tsakanin yaran.
A cewarsa, muddin ba a magance matsalar da yaran suke fuskanta a wajen neman ilimi ba, magance matsalar rashin zuwa makarantar yara zai yi wuya.
Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ne ya sanar da hakan a taron lalubo hanyoyin samun nasara da a ma’aikatar ilimi daga 2023 zuwa 2027.
Ministan ya ce shugaban kasa ya dauke ciyarwan daga hannun ma’aikatar ayyukan agaji ya dawo da shi karkashin Ma’ikatar Ilimi.