✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Malamai sun gindaya sharaɗi kafin janye yajin aiki a Abuja 

Ƙungiyar ta tabbatar da cewar sai an biya waɗanda buƙatu nata sannan za ta janye yajin aikin.

Malaman makarantu da ma’aikatan ƙananan hukumomi a Babban Birnin Tarayya, Abuja, sun bayyana cewa ba za su janye yajin aikin da suka shiga ba, har sai an biya malaman firamare bashin albashin da suke bi.

Yajin aikin ƙarƙashin jagorancin rassan ƙungiyar malamai ta ƙasa (NUT) da ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi ta ƙasa (NULGE), da na Abuja.

Wani mamba a ƙungiyar, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa shugabannin ƙungiyoyin sun bayyana wannan matsaya ne a yayin wasu taruka guda biyu da suka gudanar a ranar Alhamis da kuma Juma’ar da ta gabata.

A cewarsa, shugabannin ƙananan hukumomi guda shida a Abuja, sun roƙi shugabannin ƙungiyoyin da su dakatar da yajin aikin domin ci gaba da tattaunawa, amma taron ya kare ba tare da an cimma matsaya ba.

Ƙungiyoyin sun nuna ɓacin ransu kan yadda shugabannin ƙananan hukumomi ke karya yarjejeniyar da aka cimma a baya-bayan nan, tare da rashin damuwa da walwalar malamai da sauran ma’aikatan ƙananan hukumomi.

Ko da yake ƙungiyoyin sun yaba da matakin shugabannin wajen aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi, sun ce har yanzu akwai sauran buƙatu da ba a biya ba.

Ƙungiyoyin sun kuma amince da shawarar Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, na amfani da kashi 10 na kuɗaɗen harajin da Abuja ke tattarawa daga ƙananan hukumomi domin biyan hakkokin ma’aikatan.

Sun buƙaci a fara biyan bashin watanni takwas na sabon mafi ƙarancin albashi da malamai da ma’aikatan ƙananan hukumomi ke bi, wanda adadinsa ya kai sama da Naira biliyan 16.

Sun jadadda cewar har sai an cika waɗannan sharuɗa, sannan za su janye yajin aikin.