✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe wata mata saboda mafarki a Kano

Wasu maza su biyar sun yi taron dangi wajen kashe wata mata a dalilin mafarki da wata ta mata yi da aka ba su labarai…

An gurfanar da wasu maza su biyar kan zargin su da yin taron dangi wajen kashe wata mata saboda mafarkin da wata ta ba su labari a Jihar Kano.

Kotun Jihar Kano mai lamba 14 da ke zamanta a titin Miller ta gurfanar da su ne kan zargin hada baki da kishe matar saboda zargin ta da maita.

Mai gabatar da kara, lauyan gwamnati, Barista Lamido Abba Sorondinki ya shaida wa kotun cewa wadanda ake zargin su biyar suka hadu suka kashe wata mata mai suna Dahara Abubakar.

Barista Lamido Abba Sorondinki ya ce a garin Dadin kowa da ke Karamar Hukumar Wudil sakamakon ne wata mata mara lafiya da ta bayyana cewa ta yi mafarki cewa marigayiyar ta biyo ta da wuka.

Hakan ya sa wadana aka gurfanar suka dogara da mafarkin nata har suka yi wa marigayiya Malama Dahara Abubakar wannan danyen aikin.

Dukkanin wadanda ake zargin sun musanta laifukan da ake zargin su na hadin baki wajen aikata kisa da suka saba da sashe na 97 da 221 na Kundin Pinal Kod.

Alkalin Kotun Mai Shari’a Zuwaira Yusuf ta aike da wadanda ake zargi gidan yari ta kuma dage shari’ar zuwa ranar 16 ga watan Janairu 2024.