✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaben Kano: Yau Kotun Koli za ta saurari shari’ar Abba da Gawuna

Shari'ar Zaben Gwamnan Kano ta dauki sabon salo bayan rubutaccen hukuncin kotun daukaka kara ya ci karo da abin da aka karanta a cikin kotu.

Yau Alhamis Kotun Ƙolin Najeriya za ta yi zama kan shari’ar da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya daukaka kan taƙaddamar nasarar zaɓensa.

Abba da jam’iyyarsa ta NNPP sun ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli ne suna ƙalubalantar tabbatar ƙwace kujerarsa da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Tarayya ta yi.

Suna ƙalubalantar soke kuri’un Abba da kotun ta yi da kuma shirinta na sauya rubutaccen hukuncinta — mai karo da juna — da ya tabbatar masa da kujerar.

Shari’ar zaɓen ya ɗauki hankalin duniya ne bayan kundin hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Tarayya kan shari’ar ya fito ɗauke da saɓanin hukuncin da ta karanta a zamanta kan shari’ar da Abba Kabir Yusuf ya ɗaukaka zuwa gabanta.

A hukuncin da kotun ta karanta, ta sanar da ƙwace kujerar gwamnan a bisa hujjar cewa shi ba ɗan Jam’iyyar NNPP da ya lashe zaɓe a ƙarƙashin inuwarta ba ne, saboda babu sunansa a rajistar mambobin NNPP da jam’iyyar ta miƙa wa Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC).

Wannan wata sabuwar sarƙaƙiya ce, kasancewar a hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ta yanke a watan Satumba, ta bayyana cewa ba ta da hurumi a kan wannan zargin da Jam’iyyar APC ta yi, domin lamari ne na gabanin zaɓe.

Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta gwara kan jama’a

Amma Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta ce kotun farkon ba ta yi aikinta ba, domin kuwa tana da hurumi kan batun halascin takarar Abba a NNPP.

A saboda haka, kotun ɗaukaka ƙarar ta kwace kujerar domin, a cewarta, kujerar ba ta halasta a gare shi ba, domin kuwa INEC ba ta san shi a matsayin ɗan NNPP ba a lokacin zaɓen, don haka ba yadda za a yi ya zama ɗan takarar jami’yyar da shi ba ɗanta ba ne, ballantana ya ci mata zabe.

Sai dai kuma da kotun ta fitar da rubutaccen hukuncin, sai aka ga yana tabbatar da shi Abba a matsayin Gwamnan Kano tare da korar karar APC.

Hakan ya haifar da ruɗani da zargin maƙarƙashiyar neman sauya ainihin hukuncin.

APC na cewa kuskuren rubutu ne, NNPP kuma na cewa gaskiya ta yi bakinta — rubutaccen bayani shi ne abin dogaro — hasali ma, kundin yana ɗauke da sa-hannun magatakarda da alkalan kotun.

Lauyoyi dai sun bayyana cewa akwai tufka da warwara da kuma kura-kurai a rubutaccen hukuncin, lamarin da ya jawo kiraye-kirayen a bincika lamrin, wanda daga baya hukumar kula da shari’a (NJC) ta ce za ta bincika.

Kotun ɗaukaka karar ta bayyana cewa kuskuren rubutu aka samu a kundin hukuncin, amma hakan ba zai sauya hukuncin da ta karanta a zaman da ta yi ba.

Kotun ta kuma bayyana cewa za a iya gyara rubutaccen hukuncin bisa buƙatar bangarorin da abin ya shafa.

Daga baya ta nemi ɓangarorin su dawo da kundin hukuncin da ke hannunsu a gyara.

Amma wasu lauyoyi na bayyana cewa ba ta da hurumin yin hakan, domin lokacin da doka ta ƙayyade mata na sauraron shari’ar ya riga ya wuce.

Hakazalika wasu masana shari’a sun bayyana cewa abin da ke cikin kundin shari’ar ba kuskuren rubutu da aka sani a dokar aikin shari’a ba ne.

Wannan dambarwar dai ta haifar da zanga-zangar magoya bayan Abba da NNPP a Kano, ko da yake ’yan sanda sun hana daga baya.

NNPP da Abba dai sun ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli kan hunkuncin kwace kujerar gwamnan da kotunan farko suka yi.

Suna kuma ƙalubalantar hurumin Kotun Daukaka Kara na neman yin sauyi a rubutaccen hukuncin da ya tabbatar wa Abba kujerarsa ta Gwamnan Kano.

A halin da ake ciki wasu lauyoyin sa-kai sama da 200 sun fito za su kare Abba da NNPP a Kotun Koli domin ganin kujerarsa ta tabbata.

A daya ɓangaren kuma lauyoyi kimanin 500 ne suka ce za su kare APC da Gawuna domin ganin Abba Gida-gida ya bar gidan gwamnati ya koma gida.

Hukuncin Kotun farko

A ranar 20 ga Satumba, kotun kotu sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan Kano ta kwace kujerar Gwamna Abba bayan ta soke dubu 165 da doriya daga kuri’un da ya samu, a matsayin haramtattu, saboda rashin sa-hannu da hatimin INEC a kansu.

Hakan ya sa Gawuna ya sha gabansa a yawan kuri’u, wanda ya sa kotun ta ayyana Gawunan a matsayin halattaccen wanda ya lashe zaben, ta kuma umarci INEC ta ba shi takardar shaidar cin zabe, ta soke wanda ta ba wa Abba da farko.

Wannan hukunci ne ya sa Abba da NNPP suka garzaya zuwa Kotun Daukaka Kara ta Tarayya domin neman adalci.

Daga nan kuma suka kara daukaka kara zuwa Kotun Ƙoli, wadda suka shaida wa cewa kuri’un da APC ta tantance marasa sa-hannu da sitamfi ba su ma kai 20,000.

Don haka suna kalubalantar soke kuri’un Abba dubu 165, wanda ta ba wa Gawuna damar shan gabansa a wajen aan kuri’u.

Yanzu dai abin jira a gani shi ne yadda za ta kaya a kotun koli.