Wasu daliban jami’a da ke shirin tafiya aikin yi wa kasa hidima NYSC sun rasu a wani harin da ake zargin ’yan kungiyar asiri ne suka kai musu a yankin Gbarabtoru-Ekpetiama, Karamar Hukumar Yenagoa.
Matasan biyu da suka kammala karatunsu a Jami’ar Niger Delta (NDU), Amassomma, sun rasu ne bayan da gungun wasu mutane da ke wake-waken kungiyar asiri a cikin wata mota suka kai musu hari da adduna.
Kwamandan Kungiyar ‘Yan Banga (VGN) na Jihar Bayelsa,Tolummbofa Akpoebibo Jonathan ya ce, daya daga cikin samarin ya yi kokarin tserewa, amma maharan suka bi shi suka kama shi suka sassare shi.
Ya bayyana cewa da misalin karfe 11:00 na daren ranar Alhamis ne, abin ya faru kuma matasan biyu biyu sun mutu ne sakamakon raunukan da suka samu.
- Nijeriya ta soke ba da tallafin karatu a ƙetare
- An kama mutum 78 da makamai da kwayoyi a Kano
- JAMB ta saki sakamakon jarrabawar 2025
Kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Musa Mohammed, ya bayyana cewa an kama wasu da ake zargi kuma Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) na gudanar da bincike.
An kuma tsare direban motar da ake zargin maharan sun yi amfani da ita.