Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) ta shiga rudani a ranar Alhamis bayan da aka samu rahotanni masu karo da juna game da matsayin yajin aikin da reshenta na Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ke yi.
Shugaban Jami’ar, Farfesa Abdullahi Ibrahim Musa, ya gudanar da taron manema labarai inda ya sanar da cewa ASUU-KASU ta dakatar da yajin aikin nata, kuma za a ci gaba da karatun nan take.
Ya danganta matakin janye yajin aikin da shiga tsakani da Gwamna Uba Sani ya yi, wanda ya amince da biyan Naira miliyan 50 miliyan don walwalar ma’aikata, tare da fitar da N146 miliyan don biyan wasu albashin da aka rike da kuma alawus-alawus na shirin koyon makamar aiki na dalibai (SIWES).
Farfesa Musa ya yaba wa wadannan matakan a matsayin “jaruntaka da ba a taba gani ba,” kuma ya jinjinawa gwamnan saboda “halinsa na ban mamaki game da halin da dalibai ke ciki, yanayin ilimi, da walwalar ma’aikatan ilimi da wadanda ba na ilimi ba.”
- Layya: Farashin raguna na iya tashin gwauron zabo
- Ɗaukar fansa: Sojoji sun ragargaji Boko Haram a Dajin Sambisa
Ya kuma bayyana cewa an kafa kwamitin sasantawa karkashin jagorancin Mataimakiyar Gwamna Dokta Hadiza Balarabe, don tattaunawa da dukkan kungiyoyin jami’ar domin warware matsalolin da suka dade suna ci mata tuwo a kwarya.
Sai dai jim kadan kuma, ckin kakkausan harshe, ASUU-KASU ta musanta sanarwar Shugaban Jami’ar, inda ta bayyana ta a matsayin katsalandan kuma kuma mara izini.
A cikin wata sanarwa da Mukaddashin Shugaban kungiyar Kwamared Abubakar Abdullahi da Sakatare Kwamared Peter M. Waziri suka sanya wa hannu, kungiyar ta shawarci jama’a da su yi watsi da ikirarin da hukumar gudanarwar jami’ar ta yi.
Kungiyar ta bayyana cewa, “Ba hukumar gudanarwar Jami’ar ce ta kaddamar da yajin aikin ba, don haka ba ta da ikon dakatar da shi.”
Kungiyar ta nanata cewa har yanzu tana jiran shawarar Majalisar Zartarwarta ta Kasa (NEC) bayan taron majalisar da aka gudanar a ranar 15 ga Mayu, 2025.