✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya ɗaga darajar Kwalejin Kimiyya  ta Kabo Zuwa Jami’ar Fasaha ta Tarayya

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ɗaga darajar Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Tarayya da ke Kabo a jihar Kano, zuwa Jami'ar Kimiyya…

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ɗaga darajar Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Tarayya da ke Kabo a jihar Kano, zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Kabo.

Wannan cibiyar ilimi, wacce aka kafa a shekarar 2022, yanzu ta zama jami’a ta uku ta gwamnatin tarayya a jihar, bayan Jami’ar Bayero Kano da kuma Jami’ar Ilimi ta Tarayya da aka assasa a  kwanan nan, wacce aka sanya wa sunan marigayi Yusuf Maitama Sule.

Kano na kuma da jami’o’o’i biyu mallakin gwamnatin jiha.

Wannan ci gaban ya zo ne a daidai lokacin da ake fama da damuwa game da samar da kuɗaɗe ga manyan cibiyoyin da makarantu na gwamnati da kuma yawaitar sabbin da ake kafawa.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, wanda ya gabatar da ƙudirin dokar, ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa amincewa da ƙudirin.

A yayin zaman Majalisar Dattawa na ranar Talata, an karanta wasiƙun shugaban kasa game da kafa sabbin jami’o’i a jihohin Kano, Akwa Ibom, da Oyo.

Sanata Barau, a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashir, ya bayar, ya ce sauya fasalin ya yi daidai da kyawawan halaye na duniya a fannin ilimi kuma yana da nufin inganta samun damar yin manyan makarantu.

Ya ce: “Kafa Jami’ar Kimiyya da Kere-kere ta Tarayya ta Kabo, yana nuna jajircewar Shugaban ƙasa wajen bai wa matasan Najeriya muhimman dabarun samun ƙwarewa a fannoni irin su kere-kere da basirar na’ura da fasahar sarrafa na’ura mai kwakwalwa, da kuma an fasahar tsaron intanet.”