✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda muka fanso ’yan uwan Nabeeha daga masu garkuwa —Dangi

'Yan sanda dai yi iya bakin kokarinsu amma babu maganar cewa su ne su ka kubutar da su.

Bayanai na kara fitowa kan ’yan mata biyar ’yan gida daya da masu garkuwa da mutane suka sako a ranar Asabar da ta gabata bayan kwana 18 da sace su daga gidansu da ke Unguwar Zuma 1, a wajen garin Bwari, Abuja.

Aminiya ta ba da labarin yadda ’yan bindigar suka kashe kanen mahaifin yaran mai suna Alhaji Abdulfatah tare da jikkata ’yan sanda uku da suka je unguwar da nufin kai wa iyalin dauki bayan mahaifin ’yan matan Alhaji Mansoor Al-Kadriya ya yi wa kanin nasa bayani kan halin da suke ciki.

’Yan bindigar wadanda ke shirin barin unguwar a lokacin, sun umarci wadanda suka sato wato mai gidan da ’ya’yansa ’yan matan shida su kwanta bayan sun ji karar jiniyar motar ’yan sanda na tahowa ta inda suke, inda daga bisani suka sauya hanya suka wuce da su da misalin karfe 9:00 na dare bayan sun yi musayar wuta da ’yan sandan.

Bayan kwana uku, ’yan bindigar sun sako mahaifin, tare da umartarsa ya nemo Naira miliyan 60 zuwa ranar Juma’a 12 ga Janairu.

A yinin ne da misalin karfe 9:00 na dare suka kashe daya daga cikin ’ya’yansa mai suna Nabeeha Al-Kadriya wadda dalibar aji 4 ce a bangaren kimiyyar halittu na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya kan gaza kai kudin da mahaifin ya yi.

Sun kara adadin kudin fansar zuwa Naira miliyan 100 inda suka bashi zuwa ranar Larabar makon jiya.

A zantawarsa da Aminiya wani dan uwan mahaifiyan ’yan matan mai suna Jami’u Salman ya ce iyalan sun biya kudin fansar a ranar ta Larabar makon jiya, ya ce amma sai a ranar Asabar da ta gabata ce, daya daga cikin ’yan matan ta kira gida da misalin karfe 8:00 na dare ta sanar da cewa an sake su.

Wadanda aka sako sun hada da babbar yarsu mai suna Najeeba, wadda ’yar a ji 5 ce da ke darasin safayo da Nadheerah, ’yar aji 3 da ke darasin kula da dabbobi, dukkansu a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Sauran su ne, ’yan autan gidan wadanda tagwaye ne masu suna Habeebah da Haneesa, sai cikon ta biyar mai suna Mardeeya Isah Salahuddeen, wata danginsu da ke hutun makaranta a gidan lokacin da ’yan bindigar suka sace su daga dakinsu.

Dan uwan mahaifiyar yaran ya ce shi da wani dan uwan mahaifinsu sun je marabar Jere da ke Jihar Kaduna inda ’yan bindigar suka ce su je su kai musu kudin.

“A lokacin da muka isa wajen mun sanar da wasu sojoji da muka tarar kan abin da ya kai mu. Sojojin sun yi mana rakiya har zuwa kusa da madatsar ruwa ta Gurara inda suka tsaya.

“Daga can ne muka karasa zuwa wani daji inda mu ka dauko su, kuma sojojin suka yi mana rakiya zuwa gida inda muka iso da misalin karfe 11:00 da wasu mintoci na dare,” in ji Jami’u.

Shi ma a zantawarsa da Aminiya mutum na biyu da aka yi tafiyar da shi mai suna Mubarak Al-Kadriya wanda dan uwa mahaifin ’yan matan ne, ya musanta ikirarin da Rundunar ’Yan sandan Abuja ta yi ta hannun Babbar Jami’ar Hulda da Jama’a S.P Josephine Adeh, cewa su ne suka kubutar da yaran.

Ya ce “Sun dai yi iya bakin kokarinsu amma babu maganar cewa su ne su ka kubutar da su. Saboda har bayan biyan kudin fansar, ’yan bindigar sun ci gaba da garkuwa da su iya son ransu wato daga ranar Laraba zuwa ranar Asabar lokacin da suka ga damar sake su.

“Bayan nan sun yi ta tafiyarsu ba tare da wasu sun tunkare su da fada ba. To ka gaya mini wace irin kubutarwa ce kuma bayan an riga an biya kudin fansa,” in ji Mubarak.

Ya ce ’yan uwan nasa sun fuskanci ukuba na shafe sama da yinin ranar suna tafiya ba tare da hutu ko cin wani abinci ba, in ban da ruwan rafi da suka yi ta kwankwada kadai, kamar yadda ya yi bayani.

Ya ce ’yan bindigar sun kuma mika ’yan matan ga wasu ’yan bindiga daban da suka karasa da su zuwa inda aka dauko su.

Ya ce sun biya kudin ne cikin hadin gwiwa tare da wasu iyalai uku da aka sako mutanensu bakwai bayan sato su daga rukunin gidaje na Sagwari da ke unguwar Dutse-Makaranta a ranar Lahadi 7 ga Janairu inda suka sace mutum 10.

Aminiya ta ba da labarin cewa ’yan bindigar sun kashe Nabeeha ne tare da mutum uku daga cikin mutanen rukunin gidaje na Sagwari.

An dauko gawar mutum hudun ciki har da Nabeeha daga Babban Asibitin Umaru Musa ’Yar’aduwa da ke garin Sabon-Wuse a hanyar Abuja zuwa Kaduna tare da yi musu jana’iza a wurare da lokuta daban-daban, bayan ’yan sanda sun dauko gawarwakinsu daga kusa da wani babban titi da ke hanyar Bwari zuwa Jere inda ’yan bindigar suka kashe su.