Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa sun kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne mai suna Roland Raymond.
Cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X (Twitter), rundunar ta cafke Mista Raymond ne a ƙauyen Detti da ke Ƙaramar Hukumar Ganye ta jihar.
- An Sace Ɗalibai 2 Na Jami’ar Tarayya Ta Wukari
- Fasto mai wa’azi da macizai ya tsallake rijiya da baya
Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce, an kama Raymond a lokacin da yake ƙoƙarin karɓar kuɗin fansa.
Rundunar ‘yan sandan ta kuma ce an kama wanda ake zargin mai shekara 32 tare da haɗin gwiwar mafarauta.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Rundunar ‘yan sandan Jihar Adamawa ta kama wani Roland Raymond mai shekara 32 da haihuwa, mazaunin ƙauyen Detti, ƙaramar hukumar Ganye, bisa laifin cin zarafi mai alaƙa da garkuwa da mutane.
“An kama wanda ake zargin ne biyo bayan rahoton wasu mutane —Alhaji Yahaya Kongo da Abraham Paul — waɗanda suka bayyana cewa wanda ake zargin ya kira su ta wayar tarho ya buƙaci su biya Naira dubu 600 a matsayin kuɗin fansa.
“Bayan samun ƙorafin ne ‘yan sandan da ke yankin Ganye, tare da haɗin gwiwar mafarauta, suka yi gaggawar tattara bayanai tare da cafke wanda ake zargin a wajen karɓar kuɗin da aka nema.
“Za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu bayan bincike.”
Wannan dai shi ne karo na biyu cikin watanni biyu da jami’an tsaro za su kamo masu garkuwa da mutane a wurin karɓar kuɗin fansa.
A cikin watan Fabrairu ne dakarun bataliya ta 93 ta rundunar sojin Najeriya suka kama wata mata mai suna Janet Igohia mai garkuwa da mutane yayin karɓar kuɗin fansa a Jihar Taraba.
Sojojin sun ce an kama Igohia ne a lokacin da take ƙoƙarin karɓar kuɗin fansa a wurin ‘yan uwan wani da aka sace a Taraba suka biya.