Wani jami’in Hukumar Sibil Difens, Abubakar Abdulkadir Mayos, ya mayar da kuɗin wata maniyyaciya Naira 822,038 da suka ɓata a sansanin alhazai na Yola da ke Jihar Adamawa.
Kuɗin da aka samu sun haɗa da dala $505 da Riyal 30 na ƙasar Saudiyya, wanda ya kai kimanin Naira 822,038.
- An kama ƙasurgumin ɗan bindiga yayin tantance alhazai a Abuja
- Abba ya dakatar da hadiminsa saboda furta kalamai a kan Kwankwaso
Kuɗin mallakin Maimuna Salihu, wata maniyyaciya daga Jihar Taraba da ke shirin zuwa aikin Hajjin bana.
Jami’in ya mayar mata da kuɗin a ranar Lahadi, 18 ga watan Mayu, 2025.
An gudanar da bikin miƙa kuɗin a gaban jami’an Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ciki har da jami’in Taraba, Daraktan Tsare-tsare, da wasu manyan jami’ai.