Hedikwatar tsaro ta tabbatar da kama wasu jami’an tsaro huɗu da ke taimakawa ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.
Waɗanda ake zargin sun haɗa da wasu jami’ai biyu na rundunar haɗin gwiwa da ke aiki tare da sojoji domin yaƙar ’yan ta’addar.
A cewar Darakta mai kula da harkokin yaɗa labarai na tsaro, Manjo Janar Markus Kangye, an kame sojojin ne a wani samame da aka yi tsakanin ranakun 26 zuwa 29 ga watan Afrilu a cikin ƙananan hukumomin Bama, Kukawa, da Madagali.
Ya ce, suna daga cikin waɗanda suke taimakawa ’yan ta’adda huɗu da sojojin suka kama.
Kangye ya nuna damuwarsa kan cin amanar da suke yi, ya kuma gargaɗi kwamandojin da su wayar da kan jami’ansu kan ayyukan da za su kawo cikas ga ƙoƙarin da sojoji ke yi.
“A wani samame da aka gudanar tsakanin ranakun 26-29 ga Afrilu, 2025 a ƙananan hukumomin Bama, Kukawa, da Madagali na Jihohin Borno da Adamawa, sojoji sun kama wasu ’yan ta’adda guda huɗu da ke kai kayan aikin ga mahara, abin baƙin ciki, an tabbatar da cewa biyu daga cikinsu na cikin rundunar haɗin gwiwa.”
Don haka dole ne kwamandoji su wayar da kan jami’an rundunar haɗin gwiwa da su daina haɗa kai da wasu ko ƙarfafa ayyukan ta’addanci da ke da ikon yi wa ayyukanmu zagon ƙasa,” in ji Kangye.
A wani samame kuma, Kangye ya ce sojoji tare da haɗin gwiwar dakarun haɗin gwiwa sun kai farmakin da suka haɗa da sintiri na yaƙi, samame, da aikin share fage a ƙananan hukumomin Gwoza da Dikwa da Bama da Chibok da Gujba da Geidam da kuma Yunusari.