Rundunar ’yan sandan Jihar Adamawa ta kama wani mai suna Mohammed Umar mai shekara 19, mazaunin wata unguwa da ake kira hanyar Abuja a ƙaramar hukumar Yola ta Kudu bisa laifin sanya tufafi da shigar mata.
Kakakin rundunar ’yan sandan, SP Suleiman Ngoruje, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba ya bayyana cewa, mutumin yana ta kai-kawo a cikin harabar cocin Ngurore Lutheran Church of Christ Nigeria.
- Dangote ya sake rage farashin man fetur
- An yi Jana’izar Shugaban Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Ƙasa a Zariya
“Kamen matashi ya biyo bayan rahoton da wani mazaunin garin (da aka sakaya sunansa) ya kai hedikwatar ’yan sanda ta Ngurore, bayan ya lura da sintirin wanda ake zargin a cikin harabar cocin.”
A cewar sanarwar, Kwamishinan ’yan sandan Jihar Adamawa, Dankombo Morris, ya bayar da umarnin a mayar da batun zuwa sashin binciken manyan laifuka na Jihar, da ke Yola, domin gudanar da sahihin bincike.
“Rundunar ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaron jama’a, da zaman lafiyar jama’a da kuma ƙarfafa wa mazauna yankin gwiwa da su sanya ido tare da bayar da rahotannin wasu da ake yi zargi ga ‘yan sanda kan lokaci,” in ji shi.